Ƙarin bayani: https://hausadictionary.com/HausaRadio.net/2026-05-28
== BBCHausa Safe 2026-05-28 ==
Mai gabatarwa: Aisha Sharif Baba
#1 🎧 @0:15 Amurka da Iran sun kai wa juna hare-hare a yankin Gabas ta Tsakiya, abin da ke neman illata ƙwaryar tsagaita wuta da aka cimma.
#2 🎧 @0:24 Ƙarin hare-haren da Isra’ila ta kai sun faɗa ciki da kewen birnin Tyre da ke kudancin Lebanon, inda suka faɗa kan wani gini da ya kama da wuta daga bisani.
#3 🎧 @0:34 A Najeriya, jam’iyyar hamayya ta ADC ta bayyana sakamakon zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa, inda ta ce tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ne ya samu nasara, sai dai wasu...
#4 🎧 @1:04 Yankin Tafkin Chadi wuri ne mai albarkatun ruwa da aikin gona, amma rashin tsaro ya ci gaba da addabar al’ummar yankin.
== BBCHausa Hantsi 2026-05-28 ==
Mai gabatarwa: Aisha Sharif Baba
#5 🎧 @2:02 Maimaicin labarin ƙarin hare-haren da Isra’ila ta kai ciki da kewen birnin Tyre da ke kudancin Lebanon.
#6 🎧 @2:11 Gwamnatin Australia ta ce tana neman diyya ta kusan dala biliyan 1.5 daga katafaren kamfanin samar da kayayyakin amfani na Amurka 3M.
#7 🎧 @2:19 A Najeriya, ƙungiyoyin Fulani makiyaya sun mayar da martani kan wani rahoton Amurka da ke cewa Fulani masu ɗauke da makamai na kai hare-hare kan gonakin Kiristoci da wuraren ibada.
== BBCHausa Rana 2026-05-28 ==
Mai gabatarwa: Aisha Aliyu Jafar
#8 🎧 @3:37 Amurka ta zargi Iran da saɓa ƙa’idojin tsagaita wuta bayan da ta harba makamai zuwa Kuwait.
#9 🎧 @3:47 Gobara ta yi ajalin ɗalibai goma sha shida a wata makarantar kwana ta mata da ke Kenya.
#10 🎧 @3:59 A Najeriya, yayin da ayyukan daba ke ta’azzara a wasu sassan Arewa, musamman jihar Kano, wani babban ɗan siyasa ya shawarci ‘yan siyasa su daina bai wa matasa makamai da ƙwayoyi.
#11 🎧 @4:20 Sakamakon da aka fitar na ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC ya bar baya da ƙura, inda waɗanda suka yi rashin nasara suka yi fatali da sakamakon.
#12 🎧 @4:52 Wata ƙungiyar Fulani ta ja hankali kan yadda take cewa jami’an tsaro na ƙura wa matasan Fulani ido yayin bukukuwan Sallah.
== BBCHausa Yamma 2026-05-28 ==
Mai gabatarwa: Aisha Aliyu Jafar
#13 🎧 @5:44 Amurka ta ce ita da Iran sun amince da shirin yarjejeniyar da za ta tsawaita tsagaita wuta da suka cimma.
#14 🎧 @5:55 Firaministan Isra’ila ya bai wa sojojin ƙasar umarnin faɗaɗa mamayarsu a Zirin Gaza.
#15 🎧 @6:00 A Najeriya, ƙungiyar ƙwadago ta NLC ta koka kan yadda tattalin arziki da matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar.
#16 🎧 @6:27 Har ila yau a Najeriya, yayin da ayyukan daba ke ƙara ta’azzara a wasu sassan Arewa, musamman Kano, wani babban ɗan siyasa ya ba takwarorinsa shawara su daina ɗaure wa matasa gindi.
== DWHausa Safe 2026-05-28 ==
Mai gabatarwa: Musa Tijjani Ahmad
#17 🎧 @7:20 Rukunin farko na ‘yan ƙasar Ghana kusan ɗari uku da aka kwashe daga Afirka ta Kudu sakamakon sabbin hare-haren ƙyamar baki sun isa gida lafiya.
#18 🎧 @7:31 A ƙasashen Afirka, a duk lokacin da layya ta kama, jama’a na fuskantar matsalar tsaftar muhalli saboda datti, ledoji da jini da ake barin su a kan tituna.
#19 🎧 @7:43 Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana samun nasarar kashe ‘yan ta’adda fiye da ɗari uku da sha bakwai.
#20 🎧 @8:26 An yi musayar wuta tsakanin Amurka da Iran a kusa da Mashigar Hormuz.
#21 🎧 @8:32 Tarayyar Turai za ta faɗaɗa matakin kare tattalin arzikin ƙasashen ƙungiyar daga barazanar China.
#22 🎧 @8:38 Hukumar Lafiya ta Duniya na tafa da tashin shawo kan cutar Ebola da ke zama barazana ga harkokin kiwon lafiya a Afirka.
== DWHausa Rana 2026-05-28 ==
Mai gabatarwa: Khadija Ahmad Rufa’i
#23 🎧 @9:10 A Gabas ta Tsakiya, yayin da Iran ke kai hare-haren ramuwar gayya ga Amurka, Shugaba Trump na barazanar faɗaɗa hare-harensa kan Oman.
#24 🎧 @9:20 Tarayyar Najeriya na kashe tirilolin naira a ɓangaren hanyoyin sadarwa.
#25 🎧 @9:28 A Jamhuriyar Nijar, ana sa ran tsaro zai inganta bayan wasu matasa ‘yan daba sun amince da ajiye makamansu.
#26 🎧 @9:51 Ɗalibai da dama sun mutu sakamakon tashin gobara a wata makarantar kwana ta ƙasar Kenya.
#27 🎧 @9:56 Jagoran addinin Iran ya zargi Amurka da Isra’ila da neman durƙusar da ƙasarsa.
#28 🎧 @10:03 Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi hasashen cewa yanayin zafi zai kai ƙololo tsakanin shekaru biyar masu zuwa.
== DWHausa Yamma 2026-05-28 ==
Mai gabatarwa: Khadija Ahmad Rufa’i
#29 🎧 @10:30 A jihar Kano, yayin da ake ci gaba da dambarwar siyasa kan ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar ADC, ana kuma ci gaba da dambarwa kan masarautar jihar bayan hawan Sallah na sarakuna biyu.
#30 🎧 @10:45 A Jamhuriyar Nijar, ƙungiyoyin direbobin kabu-kabu da masu adaidaita sahu sun yi yunƙurin taimakawa wajen yaƙi da matsalar shan miyagun ƙwayoyi.
#31 🎧 @10:54 Habasha ta ɗauki matakin murƙushe ‘yan adawa saboda fargabar ɓarkewar rikici gabanin zaɓen majalisar dokokin ƙasar.
#32 🎧 @11:23 Ƙasashen Amurka da Iran sun zargi juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu.
#33 🎧 @11:29 Tsohon shugaban ƙasar Yemen, Abd Rabbu Mansur Hadi, ya rasu a ƙasar Saudiyya.
#34 🎧 @11:34 Kotun tsarin mulkin Madagascar ta yi watsi da buƙatar tsige sabon shugaban mulkin sojan ƙasar.
== RFIHausa Safe 2026-05-28 ==
Mai gabatarwa: Shamsiyya Haruna
#35 🎧 @12:08 Yayin da Amurka ta sake kai sabon hari kan sansanonin sojin Iran, rundunar juyin juya halin ƙasar ta fara mayar da martani tare da gargaɗi cikin kakkausar murya.
#36 🎧 @12:21 Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya zama halastaccen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC.
#37 🎧 @12:26 Uganda ta rufe iyakarta da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo domin kauce wa bazuwar cutar Ebola.
== RFIHausa Yamma 2026-05-28 ==
Mai gabatarwa: Ummaru Sani
#38 🎧 @12:57 Jam’iyyar adawa ta ADC ta tsayar da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar a matsayin ɗan takararta a zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe.
#39 🎧 @13:11 Jamhuriyar Nijar ta karɓi ɗaruruwan ‘yan gudun hijirar Najeriya da suka tsere wa hare-haren mayaƙan Lakurawa a wasu sassan jihar Kebbi.
#40 🎧 @13:20 Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya umurci dakarun ƙasarsa su ƙwace iko da kusan kashi saba’in na Zirin Gaza duk da yarjejeniyar tsagaita wuta.
== CRI / CGTN Hausa 2026-05-28 ==
#41 🎧 @13:58 Shugaban ƙasar Sin ya amsa wasiƙar da ɗaliban ƙasashen Sin da Amurka da ke haɗa ƙarsa da zumunta tsakaninsu suka aiko masa.
#42 🎧 @14:08 Ƙasar Sin za ta bai wa waken kofi na ƙasashen Afirka hamsin da uku damar shiga kasuwarta tun daga ranar ashirin ga watan Yuli bana.
#43 🎧 @14:13 Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Tarayyar Najeriya ya jinjina wa sadaukarwa da juriyar ‘yan Najeriya, wanda hakan a cewarsa ke haifar da sakamako mai kyau.

Comments
Nothing yet. Say the first thing.
Sign in to join the conversation.