A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya yi duba ne kan irin koma bayan da ake gani na faruwa a tsakanin tawagogin kwallon kafar Najeriya, kama daga bangaren mata mata da maza, har ma da yan wasa masu tasowa. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda ba a samun sabbin ƙasashen da ke lashe gasar kofin duniya. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...
Shirin Duniyar wasanni a wannan makon tare da Khamis Saleh ya yi duba ne a gameda nasarar da tawagar Spain ta yi kan takwararta ta Argentina a gasar cin kofin duniya karo na 23 Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali kan wasannin gab da na kusa da ƙarshe na gasar cin kofin duniya da aka kammala tsakanin ƙasashe 8 wanda kuma kawo yanzu ya rage ƙasashe 4 a wannan tafiya wadda ta faro da ƙasashe 48. A wasannin dai Faransa ta yi waje da Morocco yayinda Spain ta yi waje da Belgium kana Ingila ta yi waje da Norway yayinda Argentina mai…
Bayan nasarar da tawagogin ƙasashen Afrika 9 suka yi na kaiwa zagayen ƴan 32 a gasar lashe kofin duniya, wani lamari da ya sanya nahiyar ta kafa tarihin samun yawan wakilai a wannan zagaye, sai dai kuma ana iya cewa murna ta koma ciki domin dai tuni aka yi waje da 7 daga cikin 9. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........
Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda irin rawar da ƙasashen Afrika suka taka a wasannin rukuni a gasar lashe kofin duniya. A ƙarshen mako ne dai aka kammala wasanni rukuni, abinda ke nuna cewar an buga wasanni 72 daga cikin 104 da za a yi a wannan gasa. Sakamakon waɗannan wasani da aka yi ya nuna cewar anyi waje da tawagogin ƙasashe 16 daga cikin 48 dake fafatawa a gasar, inda ƙasashe 32…
Shirin a wannan mako zai yi duba ne kan wasu muhimman abubuwan da suka faru a gasar lashe kofin duniya ciki har da karawar da Cote d’Ivoire ta sha kashi a hannun Jamus. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.
Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako tare da Khamis Saleh ya yi duba kan irin wainar da ake toyawa a gasar nema cin kofin duniya da ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka ke karbar bakunci. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shiri........
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan gasar lashe kofin duniya da za a fara a wannan makon. Ita dai wannan gasa ta lashe kofin duniya da aka faro a shekarar 1930, Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ce ke shiryata duk bayan shekara 4, sai dai a shekarun 1942 da kuma 1946 an samu tsaikon gudanar da gasar sakamakin yaƙin duniya na biyu. Bayan kammala gasar da ƙasar Qatar ta karɓi…
Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako tare da Khamis Saleh ya yi duba kan yadda aka gudanar da wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai tsakanin ƙungiyar PSG da kuma Arsenal, inda PSG ɗin ta samu nasarar lashe gasar a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da aka ta shi 1-1. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan nasarar lashe gasar Firimiyar Ingila da Arsenal ta yi a kakar wasan bana, bayan kwashe tsawon shekaru 22 batare da tayi tozali da kofin ba. A Lahadin nan ne aka miƙawa Arsenal kofin bayan buga wasanta na ƙarshe a gasar a wannan kaka tsakaninta da Cystal Palace, inda aka tashi 2-1. Tun kafin wasan na jiya ne dai aka nasarar da Arsenal a…
Shirin Duniyar Wassani a wannan lokacin yayi duba ne kan yadda aka lashe mafi akasarin gasannin lik-lik na nahiyar Turai, in banda gasar Firimiyar Ingila. Barcelona ta lashe gasar La liga a Spain, a Inter Milan ta lashe gasar Serie A na Italiya, ita kuwa Bayern Munich ta ɗauke kofin Bundesliga na ƙasar Jamus, yayin da PSG ta lashe gasar League 1 ta Faransa. A yanzu haka dai gasar Firimiyar Ingila…
A ranar juma’ar data gabata ne dai aka kammala gasar gasar Super 4, wacce aka fafata tsakacin ƙungiyoyi 4 da suka haɗa da Sporting Lagos da Inter Lagos da Ranchers Bees ta Kaduna sai kuma Doma United, da suka zama zagaru a rukunoninsu na gasar NNL, gasa ta biyu mafi daraja a Najeriya. An gudanar da gasar ne a yanayin yadda ake gudanar da gasar lik-lik, inda kowa ya kara da kowa ganin cewa…
A wannan mako shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan halin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars ke ciki, wanda ya haddasawa ƙungiyar gagarumin koma baya. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars, ta kasance guda cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar ƙwararru da ake ji da su a shekarun baya daga yankin Arewacin Najeriya, wadda ta shafe tsawon shekaru tana…
Shirin awannan mako ya leƙa gasar Firirmiyar Najeriya ne wadda ke gab da ƙarƙarewa, amma kuma haryanzu ba a san maci tuwon ba. Yanzu haka dai an kammala wasannin mako na 35 a gasar Firimiyar Najeriya, wadda ya rage mako 3 kacal a kammala gasar a kakar wasa ta bana, amma sai dai haryanzu ƴar manuniya bata nuna ƙungiyar da za ɗauki gasar ba tsakanin ta saman teburi harzuwa wadda take a mataki na…
A makon daya gabata ne aka kammala wasannin zagayen dab dana kusa da na ƙarshe na gasar zakarun Turai, inda Bayern Munich ta cire Real Madrid, Atletico Madrid ita kuma ta doke Barcelona, Arsenal ta fidda Sporting CP, yayinda PSG ita kuma ta samu galaba kan Liverpool. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh...............
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Khamis Saley ya yi duba akan dambarwar da da ta taso dangane hukuncin karɓe nasarar Senegal ta lashe kofin Afrika na baya bayan da hukumar CAF tayi tare da maida nasarar ga ƙasar Morocco Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin........
Shirin a wannan lokaci tare da Khamis Saleh ya yi duba ne kan yadda aka kammala samun tawagogin ƙasashen da za su fafata a gasar lashe kofin duniya da ke tafe a watan Yuni mai zuwa. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin......
Shirin Duniyar Wassani a wannan lokaci yayi duba ne kan yadda Amurka ta fara gargaɗin ƴan Ghana da ke da aniyar maƙalewa idan suka je ƙasar don kallon gasar cin kofin duniya da ƙasashen Amurka da Canada da kuma Mexico za su karɓi baƙunci a watan Yuni mai zuwa. Ganin irin matakan da dama gwamnatin Amurka ke ɗauka kan shigar baki ƙasar tuni ofishin Jakadancin ƙasar da ke Ghana ya fara gargaɗin masu…
Shirin “Duniyar Wasanni” tare da Khamis Saleh a wannan lokaci zai yi duba ne kan yadda aka sanya tsarin koyar da wasan kwallon ƙafa a makarantun Boko na Jamhuriyar Nijar. A wannan makon mun yi dubi ne kan shirin koyar da wasan kwallon ƙafa da za a sirka a tsarin koyarwa a makarantun Boko a Jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarin da ake yi na haɓɓaka harkar, ganin yanda take a baya sosai a jadawalin ƙasashe da…
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali ne kan gasar tseren dawaki da aka gudanar a garin Daura da ke jihar Katsina da ke a arewacin Najeriya. A farkon watan Faburairun wannan shekarar ne aka kammala babbar gasar tseren dawaki ta ƙasa da ƙasa da ƙungiyar sukuwar dawaki ta Najeriya ke shiryawa. Wannan ne dai karo na uku da ake gudanar da irin wannan sukuwa a…
Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako, ya mayar da hankali ne kan taƙaddamar da ta dabaibaye gina filin wasa a jihar Kebbi ta arewacin Najeriya. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Khamis Saleh...
A jiya Lahadi ne dai aka buga wasan ƙarshe a gasar lashe kofin nahiyar Afrika ta AFCON karo na 35 da ƙasar Morocco ta karɓi baƙunci, inda Senegal ta samu nasara da ci 1 da nema kan Morocco, bayan da ɗan wasanta Pape Alassene Gueye ya jefa kwallo jim kaɗan bayan ƙarin lokacin. Wasan ƙarshen ya kasance mai cike da cecekuce sakamakon tsaiko minti 20 da aka samu, sanadiyar bugun daga kai sai mai…