# yadda (podcasts) — RSS Amplifier

Recent posts from the 6 feeds in the RSS Amplifier directory that cover yadda.

Page: <https://rssamplifier.com/topics/yadda/podcasts>  
Feed: <https://rssamplifier.com/topics/yadda/podcasts.md>

---

## [Me cigaban kasuwar hannayen jarin Najeriya ke nufi ga talakan ƙasar kashi na 2](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260819-me-cigaban-kasuwar-hannayen-jarin-najeriya-ke-nufi-ga-talakan-%C6%99asar-kashi-na-2?GJlXzGgqHj)

_2026-08-19 · Kasuwanci_

Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya dora kan shirin makon da ya gabata, wanda ya mayar da hankali kan ci gaba da kasuwar hannayen jarin Najeriya ta samu, wajen zama ta ɗaya a duniya, kamar yadda mujallar Bloomberg ta sanar a ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026. To amma me cikin gaban kasuwar hannayen jarin ke nufi ga takan ƙasar?

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-ECO-NIGERIA-STOCK-2026-08-19-ABBA.mp3?guid=5835a1be-9bba-11f1-9a87-557075dfb030&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda matasa suka ƙera jirgi maras matuƙi mai cin Kilomita 30 a Kano](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260818-yadda-matasa-suka-%C6%99era-jirgin-maras-matu%C6%99i-mai-cin-kilomita-30-a-kano?GJlXzGgqHj)

_2026-08-18 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin a wannan makon ya leka Kanon Najeriya, inda aka gano wani sabon tarihin bunkasar kimiyya da fasaha da matasan yankin ke jagoranta. Wannan gagarumar bajinta dai wani matashi Abubakar Waiya, wanda ya daɗe yana fafutukar kera na'urorin shawagi ne ya ƙera jirgi maras matuƙi domin taimakawa ɓangaren tsaro da kuma boma. Jirgin da ya kera a yanzu yana da ikon tashi da kansa har na tsawon kilomita…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-SCI-AND-TECH-2026-08-18.mp3?guid=206ebca2-9ade-11f1-9d85-d5a741bcbce0&source=GJlXzGgqHj)

## [Halin da ake ciki game da al'adar 'Yan Kama da ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260818-halin-da-ake-ciki-game-da-al-adar-yan-kama-da-ke-neman-%C9%93acewa-a-%C6%99asar-hausa?GJlXzGgqHj)

_2026-08-18 · Al'adun Gargajiya_

Shirin "Al’adunmu na gado, ya mayar da hankali kan fadi-tashin da ake yi don adana tsohuwar al'adar mawaƙan 'Yan Kama a ƙasar Hausa. Waƙoƙin 'Yan Kama salon fasaha ne na musamman da mawaƙan ke amfani da shi domin nishaɗantarwa, inda suke sauya shahararrun waƙoƙi su koma na maganar abinci ko cika tumbi. A cikin shirin, masana sun bayyana yadda waɗannan mawaƙa ke da ƙwarewa wajen sarrafa harshen…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-CULTURE-YAN_KAMA-NURA-2026-08-18.mp3?guid=3edc0f5e-9ada-11f1-bce7-676e6058c92c&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda wuraren saida magunguna ke samun karbuwa a jamhuriyar Nijar lokacin damuna](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260817-yadda-wuraren-saida-magunguna-ke-samun-karbuwa-a-jamhuriyar-nijar-lokacin-damuna?GJlXzGgqHj)

_2026-08-17 · Lafiya Jari ce_

Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya leƙa jamhuriyyar Nijar inda ya yi dubi kan yadda ake samun kafuwar wuraren saida magunguna birjik musamman a lokaci irin na damuna, wato dai lokacin da ake ganin yawaitar cutuka irin zazzaɓin cizon sabro. Danna alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_HEALTH-PHARMACIES_2020-08-17_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=e44df974-9a18-11f1-bb3d-111cad60ec80&source=GJlXzGgqHj)

## [Ƙarancin yashin gini na haddasa rikici tsakanin jama'a da illa ga muhalli](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260815-%C6%99arancin-yashin-gini-na-haddasa-rikici-tsakanin-jama-a-da-illa-ga-muhalli?GJlXzGgqHj)

_2026-08-15 · Muhallinka Rayuwarka_

A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan yadda aikin gine gine ke haddasa bukatar yashi wanda nemanshi ke zama matsala tsakanin jama'a, da kuma illa ga muhalli da wurin noma da hanyoyin ruwa da sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MUHALLINKA_RAYUWARKA_2026-08-15_NASIRU.mp3?guid=c0674bc6-98da-11f1-8b5c-9f95149eb222&source=GJlXzGgqHj)

## [Cigaban kasuwar hannayen jari na nufin rayuwa ta fara inganta ga talakan Najeriya?](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260812-cigaban-kasuwar-hannayen-jari-na-nufin-rayuwa-ta-fara-inganta-ga-talakan-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-08-12 · Kasuwanci_

A ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026, mujalar Bloomberg da ke bibiyar harkokin tattalin arzikin ƙasashen duniya, ta bayyana kasuwar hannayen jarin Najeriya a matsayin ta ɗaya a duniya a fannin dala, wajen yi wa ta Koriya ta Kudu fintinƙau. Masana tattalin arziki sun alakanta wannan gagarumin ci gaba da kasuwar ta samu da sauye-sauye masu tsauri da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-ECO-NIGERIA_STOCK_01-2026-08-12-ABBA.mp3?guid=97590ebc-962e-11f1-b899-f3a546cf71d4&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda cutar kwalara ta jefa ɗumbin mutane cikin firgici a jihar Bornon Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260810-yadda-cutar-kwalara-ta-jefa-%C9%97umbin-mutane-cikin-firgici-a-jihar-bornon-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-08-10 · Lafiya Jari ce_

A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan sake ɓarkewar cutar kwalara ko kuma amai da gudawa a jihar Borno, lamarin da ya jefa ɗimbin jama’a a yanayi na matuƙar damuwa damuwa musamman bayan da rahotanni ke cewa an samu yaɗuwar annobar cutar har a yankunan da ake ajje da ɗimbin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_HEALTH_CHOLERA_OUTBREAK-BORNO_2026-08-10_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=1fb14004-94a4-11f1-8a45-d3a42fe1dd18&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalli](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260808-yadda-dazuka-ke-taimakawa-wajan-kare-muhalli-1?GJlXzGgqHj)

_2026-08-08 · Muhallinka Rayuwarka_

Shirin Muhallinka rayuwarka na wannnan mako tare da Nasiru Sani ya duba irin gudun mawar da ganzun daji ke bayarwa wajan kare muhalli daga matsalar sauyin yanayi Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_ENVIRONMENT_2026-08-08_NASIRU.mp3?guid=8439a122-936b-11f1-9f3b-976cfcc5ee76&source=GJlXzGgqHj)

## [Ghana ta yiwa ƙasashen Afrika fintinkau a fannin ci gaban hada-hadar kuɗaɗe ta wayar hannu](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260805-ghana-ta-yiwa-%C6%99asashen-afrika-fintinkau-a-fannin-ci-gaban-hada-hadar-ku%C9%97a%C9%97e-ta-wayar-hannu?GJlXzGgqHj)

_2026-08-05 · Kasuwanci_

Shirin na wannan mako ya duba yadda Ƙasar Ghana ta zama jagaba a fannin hada\_hadar kuɗi ta wayar hannu a Afirka, inda a wannan shekara kaɗai kamfanonin sadarwar wayar tafi da gidanka suka yi hada-hadar sama da Cidi biliyan 40. Ku danna lamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-ECO-2026-08-05-ABBA.mp3?guid=20aeb190-90bb-11f1-a386-53b399c4dc05&source=GJlXzGgqHj)

## [Wane tasiri Chamfi ke da shi wajen gyarawa ko kuma ruguza aure musamman a zamanin baya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260804-wane-tasiri-chamfi-ke-da-shi-wajen-gyarawa-ko-kuma-ruguza-aure-musamman-a-zamanin-baya?GJlXzGgqHj)

_2026-08-04 · Al'adun Gargajiya_

Shirin Al'adunmu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan yadda Chamfe-Chamfe ke shafar lamuran auratayya musamman a zamanin baya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shrin tare da Abdullahi Isa

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_AL_ADU_CAMFE-CAMFE_2026-08-04.mp3?guid=1b70e28a-8ff2-11f1-9301-f76b6586dacb&source=GJlXzGgqHj)

## [Licensed Dispensaries, Pay with Crypto (Sponsored)](https://crawlproof.com/a/e0gPm2hSdVcE)

_2026-08-04 · **Sponsored**_

Search verified licensed dispensaries and pay with Bitcoin, Lightning, or stablecoins.

## [Yadda cutar Bilharzia ko Tsagiya ke barazana ga rayuwar ɗimbin ƴan Afirka](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260803-yadda-cutar-bilharzia-ko-tsagiya-ke-barazana-ga-rayuwar-%C9%97imbin-%C6%B4an-afirka?GJlXzGgqHj)

_2026-08-03 · Lafiya Jari ce_

A wannan makon shirin na lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba duba kan cutar Schistosomiasis (shustosumayusus) ko Bilharzia koma Snail fever kamar yadda wasu ke kiranta, cutar nan dai da aka fi sani da tsagiya a hausance, cutar alƙaluma ke nuni da cewa kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da ita na a nahiyar Afrika. Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani.......

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_HEALTH-TSAGIYA-NIGER-2026-08-03-_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=2a3be68e-8f1b-11f1-bf58-db88ccb4d9a8&source=GJlXzGgqHj)

## [Matakan da manoman Nijar ke ɗauka a lokutan da aka fuskanci ƙarancin ruwan sama](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260802-matakan-da-manoman-nijar-ke-%C9%97auka-a-lokutan-da-aka-fuskanci-%C6%99arancin-ruwan-sama?GJlXzGgqHj)

_2026-08-02 · Muhallinka Rayuwarka_

A Jamhuriyar Nijar,manoman dai sun fara da taka tsan-tsan ne saboda tsila-tsillar saukar ruwan shukar da suke fuskanta da kuma yanda ake samun dogon lokaci kafin saukar wani ruwan bayan saukar na farko, abun dake sanya shukar da suka yi ta mutu a ɗan wani lokaci.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_ENVIRONMENT_2026-08-01_NASIRU.mp3?guid=cb449ef2-8e5f-11f1-a4c7-ff4828f50443&source=GJlXzGgqHj)

## [Illar cushen kusan naira tiriliyan 1 a kasafin kuɗin Najeriya ga tattalin arziƙi](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260729-illar-cushen-kusan-naira-tiriliyan-1-a-kasafin-ku%C9%97in-najeriya-ga-tattalin-arzi%C6%99i?GJlXzGgqHj)

_2026-07-29 · Kasuwanci_

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, ya mayar da hankali ne kan yadda aka gano cushen kusan Naira triliyan ɗaya cikin kasafin kuɗin Najeriya na wannan shekarar ta 2026, domin sayen motocin alfarma da kuma ayyukan tallafa wa jama'a. Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoton da wata cibiyar da ke sa’ido kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen kasafi a Najeriya wato Tracka. Cibiyar…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-ECO-NIGERIA-2026-07-29-ABBA.mp3?guid=c629a012-8b25-11f1-8c82-592ac6ceb892&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda farashin magunguna ke tashi a lokacin damuna da aka fi fama da cutuka](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260727-yadda-farashin-magunguna-ke-tashi-a-lokacin-damuna-da-aka-fi-fama-da-cutuka?GJlXzGgqHj)

_2026-07-27 · Lafiya Jari ce_

Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi dubi ne kan yawaitar cututtuka a irin wannan lokaci na damuna, daidai lokacin da bayanai ke nuni da cewa farashin magunguna ya yi tashin gauron zabbi. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_HEALTH-PHARMACY-COST_2026-07-27_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=06dafbb8-8993-11f1-be6d-07d1b4f8dfb8&source=GJlXzGgqHj)

## [Illolin karancin gonaki kusa da jama'a da yadda ya shafi burin bunkasa samar da abinci](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260725-illolin-karancin-gonaki-kusa-da-jama-a-da-yadda-ya-shafi-burin-bunkasa-samar-da-abinci?GJlXzGgqHj)

_2026-07-25 · Muhallinka Rayuwarka_

Sau da dama, masu burin shiga harkokin noma a Nigeria kan canza tunaninsu, sakamakon rashin samun gonakin da za su noma kusa da gari, lamarin da kan tilasta su jingine aniyarsu ta yin noma. Gwamnatin Nigeria dai, ta sha kira ga ‘yan kasar da su koma gona, la’akari da yadda Allah ya albarkaci kasar da wadatattun filayen noma da kuma yanayi mai kyau da za a iya noma kowane irin nau’in kayan abinci.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/environ_saturd.mp3?guid=f7ae9224-885e-11f1-acb5-9f65143c79d8&source=GJlXzGgqHj)

## [Matakin matatar Ɗangote ya fusata ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260722-matakin-matatar-%C9%97angote-ya-fusata-%C6%99ungiyar-dillalan-man-fetur-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-22 · Kasuwanci_

Shirin a wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi dubi ne kan matakin da ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta sanar na dakatar da sayen mai daga matatar Dangote, sakamakon matakin da matatar ta ɗauka na fara sayar musu da man da take tacewa da dala maimakon Naira. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-ECO-2026-07-22-ABBA.mp3?guid=4d02caa6-85bc-11f1-b633-d112579d0824&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda gwamnatin Kano ta yi nasarar rage mace-macen mata a lokacin haihuwa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260720-yadda-gwamnatin-kano-ta-yi-nasarar-rage-mace-macen-mata-a-lokacin-haihuwa?GJlXzGgqHj)

_2026-07-20 · Lafiya Jari ce_

Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan nasarar da jihar Kano ke iƙirarin samu bayan fitar wani rahoto da ke cewa an samu raguwar mace-macen mata a lokacin haihuwa a sassan jihar wadda a baya ke sahun gaba wajen asarar rayukan ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko goyon ciki Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin..........

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_HEALTH-MATERNAL_MORTALITY_2026-07-20_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=b4244128-8423-11f1-a592-7d8e98d13a62&source=GJlXzGgqHj)

## [Makomar ilimin yara a Kano na cikin halin rashin tabbas](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260714-makomar-ilimin-yara-a-kano-na-cikin-halin-rashin-tabbas?GJlXzGgqHj)

_2026-07-14 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin na wannan makon cigaba ne kan wanda muka gabatar a makon jiya, wanda ya gano yadda yara a wasu yankunan jihar Kano basa zuwa makaranta saboda yawon tallace-tallace domin tara kudin kayan ɗaki. Yayin da su kuma mazan suke diban yashi da fasa Dutse, da sunan wai su taso suna da sana'ar dogaro da kai. Yankunan da wannan lamari yafi kamari sun hada da Challawa, Kafin Maiyaki, Madobi, Gora, da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-SCI-AND-TECH-2026-07-14.mp3?guid=471fafce-7f62-11f1-a08a-45e43ba2eff1&source=GJlXzGgqHj)

## [Muhimmancin zurfafa bincike a dukkan fannoni gabanin aure](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260714-muhimmancin-zurfafa-bincike-a-dukkan-fannoni-gabnin-aure?GJlXzGgqHj)

_2026-07-14 · Al'adun Gargajiya_

Shirin 'Al'adunmu Na Gado zai yi duba ne kan muhimmancin zurfafa bincike gabanin aure. Al’adun al’ummar Hausawa da ma mafi yawan al’ummomin da ke zaune a yankin arewacin Nigeria, sun sahale wa iyaye, gudanar da bincike kan yaron da ya nuna kai yana son ‘yarsu da aure, kamar yadda shima bangaren angon, kan yi bincike kan yanayin lafiya, tarbiyya da nasabar yarinyar. Irin wannan bincike, ya taimaka…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_AL_ADU_-BICINKE_KAFIN_AURATAR_DA_YA_A_2026-07-14.mp3?guid=dacbce80-7f60-11f1-bf2b-1dab813a2f24&source=GJlXzGgqHj)

## [Matsalar ƙarin mahaifa ko fibroids ga lafiyar mata](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260713-matsalar-%C6%99arin-mahaifa-ko-fibroids-ga-lafiyar-mata?GJlXzGgqHj)

_2026-07-13 · Lafiya Jari ce_

Shirin Lafiya Jari Ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar ƙaba ko ƙarin mahaifi ko kuma fibroids da ke addabar tarin mata ta yadda da dama ke rayuwa da shi ba tare da sani ba, yayinda wanzuwarsa a mahaifa kan haddasa matsala ga yanayin haihuwa ga matan. Galibi mata a tsakanin shekaru 35 zuwa 37 ne suka fi kamuwa da wannan lalura ta Fibroids, a wani yanayi da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_HEALTH-WOMEN_FIBROIDS-2026-07-13_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=90130864-7ea1-11f1-89b1-d560f093ee90&source=GJlXzGgqHj)

## [Ask the crowd: AI or not (Sponsored)](https://crawlproof.com/a/gey4Ol60z1pb)

_2026-07-13 · **Sponsored**_

Get a transparent verdict from verified humans via web, RSS, or API.

## [Rashin rassan bankuna ya tilastawa al'ummar karkara rungumar POS a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260708-rashin-rassan-bankuna-ya-tilastawa-al-ummar-karkara-rungumar-pos-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-08 · Kasuwanci_

Shirin kasuwa akai miki dole dake bibiyar harkokin kasuwanci da tattalin arziki na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ci gabar fasahar zamani da aka samu a fannonin haɗar-haɗur ƙudi a Najeriya, ke shafar al’ummomi a yankunan ƙarƙara.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-ECO-2026-07-8-ABBA.mp3?guid=fcec10f0-7abb-11f1-8ee7-4bd5fac9b0c9&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda makomar ilimin yaran karkara a Najeriya ke cikin rashin tabbas](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260708-yadda-makomar-ilimin-yaran-karkara-a-najeriya-ke-cikin-rashin-tabbas?GJlXzGgqHj)

_2026-07-08 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A wannan makon, shirin ya nufi yankunan karkara, inda inda gine-ginen makarantu ke ci gaba da kasancewa a matsayin kango, kasancewar babu dalibai. A wasu wuraren kuma, azuzuwan sun zama fanko, yayin da matasa da yara suka ƙaurace wa shiga, ‘yan mata na fita birni yin tallace-tallace, su kuma samari na dambatawa da aikin ƙwadagon fasa duwatsu da ɗiban yashi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-SCI-AND-TECH-2026-07-07.mp3?guid=4df503e4-7abc-11f1-ad90-8115b569da94&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda cutar Typhiod ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a Afirka da Asiya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260706-yadda-cutar-typhiod-ke-barazana-ga-rayuwar-miliyoyin-mutane-a-afirka-da-asiya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-06 · Lafiya Jari ce_

Shirin na Lafiya Jari ce zai a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan zazzaɓin Typhoid, cuta mai haɗari wadda ƙwayar cutar Salmonella Typhi ke haddasawa, inda ta kan yaɗu ta hanyar abinci ko ruwan da ya gurɓata. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_HEALTH-TYPHOID_FEVER-2026-07-06_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=fc6d962a-791d-11f1-9877-6d2c5b2cd760&source=GJlXzGgqHj)

## [Ana samun ƙaruwar cin bashin kuɗin kiran waya tsakanin jama'ar Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260701-ana-samun-%C6%99aruwar-cin-bashin-ku%C9%97in-kiran-waya-tsakanin-jama-ar-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-01 · Kasuwanci_

Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan Najeriya suka rungumi ɗaukar bashin kiran waya, wanda wani rahoto ya ce, a bara kaɗai anci bashin kiran waya da ƙudinsu ya kai Naira Tiriliyan 4 da biliyan 61. Wasu bayanai da cibiyar fintech firms Optasia mai tattara alƙaluman shige da ficen kuɗaɗen layukan sadarwa ta fitar a baya-bayan nan, ya…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-ECO-AIRTIME-2026-07-01-ABBA.mp3?guid=1d148780-752c-11f1-ab18-ad9b86483aa0&source=GJlXzGgqHj)

## [Makomar makarantun gwaji na harsunan gida a Jamhuriyar Nijar.](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260630-makomar-makarantun-gwaji-na-harsunan-gida-a-jamhuriyar-nijar?GJlXzGgqHj)

_2026-06-30 · Al'adun Gargajiya_

Shirin wannan makon zai duba makomar makarantun gwaji na harsuna gida da suka haɗa harshen Hausa. A waɗannan makarantu, za a riƙa koyarwa da harsunan gida. Za a koya wa yara sana'o'i irin na gargajiya, a kuma koya musu adabin harsshe da sauransu.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_TASIRIN_MAKARANTU_A_HARSHEN_HAUSA_2026-06-29.mp3?guid=d269c5d4-746c-11f1-8c22-432894e2c7a6&source=GJlXzGgqHj)

## [Taron ƙaddamar da littafin tarihi na wani fitaccen matashi a Kanon Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260630-taron-%C6%99addamar-da-littafin-tarihi-na-wani-fitaccen-matashi-a-jiha-kano?GJlXzGgqHj)

_2026-06-30 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan taron ƙaddamar da sabon littafin tarihin nan mai suna 'Mu San Magabata', wanda fitaccen matashin marubuci Kabiru Ahmad Kwalli ya rubuta da aka gudanar a jihar Kanon Najeriya. Taron ya haɗa masana, sarakuna, da ɗandazon al'umma domin duba yadda za a ceto tarihin ƙasar Hausa da ke shirin bacewa. Wannan littafi, kamar yadda masana da dama suka bayyana,…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SCI-AND-TECH-2026-06-30.mp3?guid=42c72b3a-746a-11f1-8632-8da6f2af1ad5&source=GJlXzGgqHj)

## [Ƙaruwar masu fama da cutar sikila a Jamhuriyar Kamaru](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260629-%C6%99aruwar-masu-fama-da-cutar-sikila-a-jamhuriyar-kamaru?GJlXzGgqHj)

_2026-06-29 · Lafiya Jari ce_

A wannan makon shirin ya yi duba ne kan ƙaruwar masu fama da cutar sikila a jamhuriyyar Kamaru bayan fitar wani rahoto da ke cewa cikin shekara 1 kaɗai an tattara alƙaluman sabbin mutum dubu 6 da aka gano suna ɗauke da cutar. Wannan cuta mai alaƙa da nau’in jini, na daga cikin matakan yaƙi da ita shi ne tabbatar da gwaje-gwajen jini tun kafin aure don kaucewa haifar yara masu ɗauke da ita, ganin…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_HEALTH-CAMEROON-SICKLE_CELL_2026-06-29_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=9d2cbfb0-73aa-11f1-b4a2-0934dbde6202&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda Hausawa ke cin kasuwar abincin gargajiya a Saudiyya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260623-yadda-hausawa-ke-cin-kasuwar-abincin-gargajiya-a-saudiyya?GJlXzGgqHj)

_2026-06-23 · Al'adun Gargajiya_

Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoullaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda Hausawa ke ɗabbaƙa al'adunsu ta hanyar hada-hadar abincin gargajiya a ƙasa mai tsarki ko kuma Saudi Arabiya. Kamar yadda ya ke sanannen abu, Hausawa kan rungumi mabanbantan sabbin al'adu amma yana matuƙar wahala a garesu su yi watsi da abincin da suturarsu, wannan ya sanya samun kasuwannin abincin gargajiya da dama…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_HAUSA_ALIMENTATION_IN_SDAUDIYYA-AL_ADU_2026-06-23_wav.mp3?guid=aab766be-6ef3-11f1-b228-7df663847292&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda aka gudanar da taron manyan masana na duniya a birnin Lagos](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260623-yadda-aka-gudanar-da-taron-manyan-masana-na-duniya-a-birnin-lagos?GJlXzGgqHj)

_2026-06-23 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A wannan makon, shirin ya mayar da hankali ne kan babban taron ƙungiyar Lagos Studies Association karo na goma da aka kammala a ƙarshen mako, wanda ya saba haɗa masana, malaman jami'o'i, da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje domin tattauna halin da ilimi yake ciki a nahiyar Afirka cikin wannan ƙarni. Wannan taro, wanda aka kafa shi shekaru goma da suka gabata a birnin…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SCI-AND-TECH-2026-06-23.mp3?guid=0bed7bfe-6ee4-11f1-b94e-ed9400012577&source=GJlXzGgqHj)

## [Matsalar ambaliyar ruwa da kan dagula lamuran al’uma a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260620-matsalar-ambaliyar-ruwa-da-kan-dagula-lamuran-al-uma-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-06-20 · Muhallinka Rayuwarka_

Kamar kowace shekara, a bana ma ana hasashen samun ambaliyar ruwa a wasu ƙasashen yammacin Afrika, inda akan samu rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa. A Najeriya, an sha samun hasarar rayuka a sanadin matsalar ambaliyar ruwan, da kan rutsa da wasu yankunan ƙasar.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_ENVIRONMENT_2026-06-20_NASIR.mp3?guid=15ab0c30-6cda-11f1-b3a8-87bcfc211ad9&source=GJlXzGgqHj)

## [Trade Smarter With IBKR (Sponsored)](https://crawlproof.com/a/itvEqSuLodqE)

_2026-06-20 · **Sponsored**_

Join Interactive Brokers through a referral and start investing with low-cost global access.

## [Yadda tattalin arzikin Ghana ke haɓɓaka sannu a hankali](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260617-yadda-tattalin-arzikin-ghana-ke-ha%C9%93%C9%93aka-sannu-a-hankali?GJlXzGgqHj)

_2026-06-17 · Kasuwanci_

Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane yadda tattalin arzikin ƙasar Ghana ke ci gaba da ɓunƙasa sannu a hankali. Ku danna alamar sauraro domin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-ECO-GHANA-2026-06-17-ABBA.mp3?guid=1b9f86f8-6a27-11f1-a907-5565451e5dd3&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda kiɗan Gurmi ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260616-yadda-ki%C9%97an-gurmi-ke-neman-%C9%93acewa-a-%C6%99asar-hausa?GJlXzGgqHj)

_2026-06-16 · Al'adun Gargajiya_

Shirinmu na yau ya leƙa sassan arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da duba yadda wani fitaccen kiɗan gargajiya, wato kiɗan Gurmi, ke fuskantar barazanar bacewa a fadin ƙasar Hausa. Shin me ke janyo haka, kuma wane canji fasahar zamani ta kawo? Gurmi, kayan kiɗa ne da aka sani tun kaka da kakanni, wanda ƙera ta hanyar amfani da ƙoƙon ƙwarya da aka rufe shi da fatar dabba, musamman fatar…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_AL_ADU_GURMI-_2026-06-16__EDITED.mp3?guid=a609a4dc-6963-11f1-883b-2962102ed5b9&source=GJlXzGgqHj)

## [Masana na ci gaba da tsoratar da al'umma game da illolin da ke tattare da gurɓatacciyar iska](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260613-masana-na-ci-gaba-da-tsoratar-da-al-umma-game-da-illolin-da-ke-tattare-da-gur%C9%93atacciyar-iska?GJlXzGgqHj)

_2026-06-13 · Muhallinka Rayuwarka_

A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan tasirin gurɓatacciyar iska ga lafiyar halittu da muhalli wato air pollution a turance. Iska na gurɓa ta ne ta hanyoyi da dama, kama daga hayaƙin na’urori wato injina a masana'antu, zuwa tarkacen bola ko kuma ƙone wasu abubuwa, wanda su ke kawo cikas ga yanayin muhalli tare kuma da kawo tazgaro ga lafiyar ɗan Adam.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_ENVIRONMENT_2026-06-13_NASIRU.mp3?guid=72bf283c-675f-11f1-80b2-415b24a3f3ce&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da gagarumin taron sada zumunci](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260609-yadda-hausawa-mazauna-jamus-suka-gudanar-da-gagarumin-taron-sada-zumunci?GJlXzGgqHj)

_2026-06-09 · Al'adun Gargajiya_

Shirin Al'adun mu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da wani gagarumin taro. Ku danna alamar Saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_AL_ADU_RANAR_HAUSA_A_JAMUS_2026-06-09.mp3?guid=8e023626-63df-11f1-a5a5-7be3d85db93d&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda talauci ke hana ɗalibai cikar burinsu](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260609-yadda-talauci-ke-hana-%C9%97alibai-cikar-burinsu?GJlXzGgqHj)

_2026-06-09 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi hasken rayuwa na wanna Mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsin tattalin arziki ke tilstawa ɗalibai haƙura da cikar burinsu na karatu, don kawai neman abin kaiwa baka, a kowacce rana. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsioyya Haruna.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-CI-AND-TECH-2026-06-09.mp3?guid=e91467ec-63de-11f1-afbf-7be3d85db93d&source=GJlXzGgqHj)

## [Illolin da ke tattare da sauya launin fata da wasu mata ke yi](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260608-illolin-da-ke-tattare-da-sauya-launin-fata-da-wasu-mata-ke-yi?GJlXzGgqHj)

_2026-06-08 · Lafiya Jari ce_

Shirin lafiya Jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda mata suka rungumi tsarin gyaran jiki ta fannoni daban-daban kama daga magungunan sha ko mayukan shafawa ko kuma salon amfani da na’ura da nufin ƙawata sura. Wasu daga cikin batutuwa mafi jan hankali a wannan babi na gyaran jiki shi ne tayar da komaɗar fata da sauran sassan jiki don killacewa ko kuma kange kai daga bayyanar tsufa,…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_HEALTH_SKIN_BLEACHING_RISK_TO_HEALTH_2026-06-08_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=30ebe1e6-631f-11f1-b1ca-7510bbe397aa&source=GJlXzGgqHj)

## [Kananan manoma a Najeriya na nan kan tsarin noma na kaka da Kakanni](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260606-kananan-manoma-a-najeriya-na-nan-kan-tsarin-noma-na-kaka-da-kakanni?GJlXzGgqHj)

_2026-06-06 · Muhallinka Rayuwarka_

A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan yadda har yanzu, kananan manoma a Nigeria na nan kan tsarin noma na Kaka da Kakanni, lamarin da ake gani yana hana ruwa gudu wajen tabbatar da cimma burin kasar na kasancewa mai dogaro da-kai a fannin samun wadatar abinci.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_ENVIRONMENT_2026-05-23_NASIRU.mp3?guid=ac46bd10-61d6-11f1-b755-4d5b2ffc4f51&source=GJlXzGgqHj)

## [Shirin kawar da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta na samun nasara a Jigawa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260602-shirin-mayar-da-yaran-da-ba-sa-zuwa-makaranta-ajujuwa-na-samun-kar%C9%93uwa-a-jihar-jigawa?GJlXzGgqHj)

_2026-06-02 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya sake waiwayar matsalar nan ce ta yawaitar yaran da ba za zuwa makaranta a arewacin Najeriya, batun da a fannin ilimi ke ci wa al’ummar yankin tuwo a ƙwarya. Masu iya magana dai na cewa ‘mai rai ba ya rasa motsi’ domin kuwa duk da girman da wannan matsala ta yi a Najeriya musamman ma yankin arewacin ƙasar, akwai waɗanda suka tashi tsaye wajen ganin sun…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SCI_AND_TECH-NURA-2026-01-02.mp3?guid=2de1bef4-5e69-11f1-8a60-7567fe6d1d99&source=GJlXzGgqHj)

## [Illolin magungunan matsi ga lafiyar mata](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260601-illolin-magungunan-matsi-ga-lafiyar-mata?GJlXzGgqHj)

_2026-06-01 · Lafiya Jari ce_

Shirin a wannan mako zai ɗora ne akan wanda ya gabace shi a makon jiya, sai dai a wannan karon zamu karkata ga illolin da magungunan matsi ke haifarwa ga lafiyar mata, duk da ya ke matan kan yi don bajinta ko nuna isa a wajen mazajensu. Danna alamar sauti don sauraron karin bayani.....

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_HEALTH-WOMEN-INSERT_2026-06-01_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=6b63d08c-5d97-11f1-b6ea-e5f480bc3bb8&source=GJlXzGgqHj)

## [Gombe: Fulani sun yi taro kan warware matsalolin da ke ɓata musu suna](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260528-gombe-fulani-sun-yi-taro-kan-warware-matsalolin-da-ke-%C9%93ata-musu-suna?GJlXzGgqHj)

_2026-05-28 · Al'adun Gargajiya_

Shirin Al'adunmu na Gado a wannan mako, yayi tattaki ne zuwa garin Gombe, inda Al'ummar Fulani suka gudanar da wani taro na farfaɗo da Al'adunsu na Gargajiya, da kuma tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi wajen maido da Tarbiyya, gami da zamantakewa kyakkyawa a tsakanin Fulanin da kuma sauran Ƙabilu.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG_AL_ADU_2026-05-26.mp3?guid=ed37015a-5aaf-11f1-b034-0dd788dec897&source=GJlXzGgqHj)

## [Abubuwan da ke haddasa cutuka ga al'aura ko matantaka ga mata](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260525-abubuwan-da-ke-haddasa-cutuka-ga-al-aura-ko-matantaka-ga-mata?GJlXzGgqHj)

_2026-05-25 · Lafiya Jari ce_

Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon ya yi nazari kan ƙaruwar matan da ke fama da cutuka masu alaƙa da al’aura ko kuma matantaka, tare da laluben hanyoyin magancesu ta hanyar tattaunawa da ƙwararru a wannan fanni, cutukan da ƙwararrun ke alaƙantawa da rashin baiwa al’aurar kariya wanda a lokuta da dama ke haddasa gagarumar matsala. Ku lasha alamar sauti don sauraron shirin tare da Azima Bashir…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG_HEALTH-VAGINAL_INFECTION_2026-05-25_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=a95f1e56-581e-11f1-b0cd-05bf8ed4411d&source=GJlXzGgqHj)

## [Yawaitar takin jabu ya zamewa Manoman Najeriya ƙalubale a bana](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260523-%C9%93azuwar-takin-zamani-da-magungunan-feshin-%C6%99wari-da-na-ciyawa-na-jabu-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-05-23 · Muhallinka Rayuwarka_

Shirin 'Muhallinka Rayuwarka na wannan makon, ya tattauna ne da masu ruwa da tsaki kan sha'anin Noma, a kan matsalar yawaitar taki da kuma magungunan ƙwari na jabu, matsalar da ta zamewa manoman Najeriya ƙalubale babba a shekarar bana.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG_ENVIRONMENT_2026-05-23_NASIRU.mp3?guid=509acb0e-56d8-11f1-9602-812a22eed23f&source=GJlXzGgqHj)

## [Koken ƴan Najeriya kan yadda bankuna ke zare musu kuɗi daga asusun ajiyarsu](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260520-koken-%C6%B4an-najeriya-kan-yadda-bankuna-ke-zare-musu-ku%C9%97i-daga-asusun-ajiyarsu?GJlXzGgqHj)

_2026-05-20 · Kasuwanci_

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan yadda ƴan Najeriya, ke nuna fushinsu dangane da zargin cire musu kuɗi ba bisa ka’ida ba daga asusun bankunansu. Miliyoyin 'yan Najeriya da yanzu haka ke fuskantar hauhawan farashin kayayyaki da kuɗin sufuri, da kuma rashin tabbas ga makomarsu a fannin tattalin arziki, caje-caje da dama da bankuna ke yi a asusun…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG-ECO-BANKS-2026-05-20-ABBA.mp3?guid=7af69ff0-5425-11f1-b27f-d134e770dae5&source=GJlXzGgqHj)

## [Ɗimbin matasa na haƙura da karatun boko saboda rashin tabbas kan samun aiki](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260519-%C9%97imbin-matasa-na-ha%C6%99ura-da-karatun-boko-saboda-rashin-tabbas-kan-samun-aiki?GJlXzGgqHj)

_2026-05-19 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matasa a baya-bayan na ke haƙura da ilimin boko saboda shakku kan yiwuwar samun aikin yi. Matsalar rashin aikin yi bayan shafe tsawon shekaru ana karatu tare da kashe maƙuden kuɗaɗe ya sanya matasa da dama musamman waɗanda ba ƴaƴan wasu ba ajje tunanin karatu tare da mayar da hankali a kasuwanci da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG-SCI_AND_TECH.mp3?guid=d2398d58-535e-11f1-a9c2-f70a09b3638e&source=GJlXzGgqHj)

## [Abubuwan da ya kamata a sani kan sabuwar cutar Hantavirus da ta ɓulla](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260518-abubuwan-da-ya-kamata-a-sani-kan-sabuwar-cutar-hantavirus-da-ta-%C9%93ulla?GJlXzGgqHj)

_2026-05-18 · Lafiya Jari ce_

Shirin Lafiya Jari Ce a wannan makon ya yi nazari kan cutar Hantavirus da duniya ta ga ɓullarta a baya-bayan nan, lamarin da ya sanya fargaba a zuƙatan jama’a, musamman ganin yadda ake alaƙanta wannan cuta a sahun masu haɗari da tarihi ya nuna yaddda suka yiwa duniya ɓarna matuƙa. Cikin watan jiya ne aka ga ɓullar wannan cuta a wani jirgi da ya taso daga Argentina zuwa Cape Verde, sai dai tilas ya…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG_HEALTH-HANTAVIRUS_OUTBREAK-2026-05-18_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=8fe1453c-5295-11f1-aaba-fb0fdf091f90&source=GJlXzGgqHj)

## [Sauyin Yanayi ya jefa Manoma cikin ruɗani kan lokacin da ya dace su fara shuka](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260516-ruwan-sama-na-farko-ya-jefa-manoma-a-jihohin-arewacin-najeriya-cikin-ru%C9%97ani-da-fargaba?GJlXzGgqHj)

_2026-05-16 · Muhallinka Rayuwarka_

Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna na a kan yadda samun saukar Ruwan Sama na farko a bana ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani dangane da lokacin da ya dace su fara shuka. Wannan na zuwa ne a yayin da hukumar hasashen Yanayi ta Najeriya wato NIMET, da uma wasu masana ke gargaɗi game da yiwuwar ɗaukewar ruwan saman da wuri, lamarin da zai yi janyo tafka…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG_ENVIRONMENT_2026-05-09_NASIRU.mp3?guid=806d6e1a-514a-11f1-a030-e79a08f1d82a&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda ƴan kasuwa a Najeriya suka jingine harakokinsu saboda tsadar sufuri](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260513-yadda-%C6%B4an-kasuwa-a-najeriya-suka-jingine-harakokinsu-saboda-tsadar-sufuri?GJlXzGgqHj)

_2026-05-13 · Kasuwanci_

Shirin Kasuwa akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG-ECO-BAUCHI-2026-05-13-ABBA.mp3?guid=0c89d0a2-4eb0-11f1-aecc-6f5775d05658&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda tsadar sufuri ya tilastawa 'yan kasuwa jingine sana'o'insu a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260513-yadda-tsadar-sufuri-ya-tilastawa-yan-kasuwa-jingine-sana-o-insu-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-05-13 · Kasuwanci_

A yau shirin ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Sannu a hankali, irin hada-hadar da aka saba gani tsakanin mafi yawan kasuwannin Nigeria na neman zama abun tarihi, sakamakon yadda ‘yan kasuwa masu tarin yawa suka jingine harkokinsu na kasuwanci saboda…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG-ECO-BAUCHI-2026-05-13-ABBA.mp3?guid=a7ecbb90-4eab-11f1-a2f6-5ba96e39cc49&source=GJlXzGgqHj)

## [An yafe wa ɗaliban da ke son shiga kwalejin ilimi rubuta JAMB a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260512-an-yafe-wa-%C9%97aliban-da-ke-son-shiga-kwalejin-ilimi-rubuta-jamb-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-05-12 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A yau muna ɗauke da wani labari mai daɗi ga ɗaliban da ke sha’awar zama malamai da kuma masu son shiga Kwalejin Ilimi a faɗin Najeriya. Gwamnatin ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin sauƙaƙa wa ɗalibai hanyar neman ilimi da kuma ƙarfafa musu gwiwa ta fuskar kuɗi. Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya sanar da cewa ɗaliban da ke son shiga Kwalejin Ilimi yanzu ba sai sun rubuta jarrabawar UTME ba.…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG-SCI-AND-TECH-2026-05-12.mp3?guid=9d1f2112-4ded-11f1-aa3f-5552ca60e7a4&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda al'ummar wani gari suka riƙe Al'adar da suke kira da "Sai kowa ya zo"](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260512-yadda-al-adar-sai-kowa-ya-zo-ke-samun-%C6%99arbuwa-a-arewacin-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-05-12 · Al'adun Gargajiya_

Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako tare da Abdoulaye Issa ya yi duba kan wata Al'ada da ake kira "sai kowa ya zo" a tsakanin al'ummar wani gari da ke Yankin Arewacin Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani.......

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG_AL_ADU_SAI_KA_ZO_2026-05-12___OK_wav.mp3?guid=407388ec-4de1-11f1-81c5-c5cc1f66516a&source=GJlXzGgqHj)

