# shirin (audio feeds) — RSS Amplifier

Recent posts from the 8 feeds in the RSS Amplifier directory that cover shirin.

Page: <https://rssamplifier.com/topics/shirin/audio>  
Feed: <https://rssamplifier.com/topics/shirin/audio.md>

---

## [Yadda matasa suka ƙera jirgi maras matuƙi mai cin Kilomita 30 a Kano](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260818-yadda-matasa-suka-%C6%99era-jirgin-maras-matu%C6%99i-mai-cin-kilomita-30-a-kano?GJlXzGgqHj)

_2026-08-18 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin a wannan makon ya leka Kanon Najeriya, inda aka gano wani sabon tarihin bunkasar kimiyya da fasaha da matasan yankin ke jagoranta. Wannan gagarumar bajinta dai wani matashi Abubakar Waiya, wanda ya daɗe yana fafutukar kera na'urorin shawagi ne ya ƙera jirgi maras matuƙi domin taimakawa ɓangaren tsaro da kuma boma. Jirgin da ya kera a yanzu yana da ikon tashi da kansa har na tsawon kilomita…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-SCI-AND-TECH-2026-08-18.mp3?guid=206ebca2-9ade-11f1-9d85-d5a741bcbce0&source=GJlXzGgqHj)

## [Halin da ake ciki game da al'adar 'Yan Kama da ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260818-halin-da-ake-ciki-game-da-al-adar-yan-kama-da-ke-neman-%C9%93acewa-a-%C6%99asar-hausa?GJlXzGgqHj)

_2026-08-18 · Al'adun Gargajiya_

Shirin "Al’adunmu na gado, ya mayar da hankali kan fadi-tashin da ake yi don adana tsohuwar al'adar mawaƙan 'Yan Kama a ƙasar Hausa. Waƙoƙin 'Yan Kama salon fasaha ne na musamman da mawaƙan ke amfani da shi domin nishaɗantarwa, inda suke sauya shahararrun waƙoƙi su koma na maganar abinci ko cika tumbi. A cikin shirin, masana sun bayyana yadda waɗannan mawaƙa ke da ƙwarewa wajen sarrafa harshen…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-CULTURE-YAN_KAMA-NURA-2026-08-18.mp3?guid=3edc0f5e-9ada-11f1-bce7-676e6058c92c&source=GJlXzGgqHj)

## [Manyan kalubalen da tawagogin ƙwallon ƙafar Najeriya ke fuskanta a harakar wasanni](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/wasanni/20260817-manyan-kalubalen-da-tawagogin-%C6%99wallon-%C6%99afar-najeriya-ke-fuskanta-a-harakar-wasanni?GJlXzGgqHj)

_2026-08-17 · Wasanni_

Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya yi duba ne kan irin koma bayan da ake gani na faruwa a tsakanin tawagogin kwallon kafar Najeriya, kama daga bangaren mata mata da maza, har ma da yan wasa masu tasowa. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/sports_15.mp3?guid=159858a2-9a1a-11f1-9eb8-33840bc1377b&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda wuraren saida magunguna ke samun karbuwa a jamhuriyar Nijar lokacin damuna](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260817-yadda-wuraren-saida-magunguna-ke-samun-karbuwa-a-jamhuriyar-nijar-lokacin-damuna?GJlXzGgqHj)

_2026-08-17 · Lafiya Jari ce_

Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya leƙa jamhuriyyar Nijar inda ya yi dubi kan yadda ake samun kafuwar wuraren saida magunguna birjik musamman a lokaci irin na damuna, wato dai lokacin da ake ganin yawaitar cutuka irin zazzaɓin cizon sabro. Danna alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_HEALTH-PHARMACIES_2020-08-17_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=e44df974-9a18-11f1-bb3d-111cad60ec80&source=GJlXzGgqHj)

## [Ƙarancin yashin gini na haddasa rikici tsakanin jama'a da illa ga muhalli](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260815-%C6%99arancin-yashin-gini-na-haddasa-rikici-tsakanin-jama-a-da-illa-ga-muhalli?GJlXzGgqHj)

_2026-08-15 · Muhallinka Rayuwarka_

A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan yadda aikin gine gine ke haddasa bukatar yashi wanda nemanshi ke zama matsala tsakanin jama'a, da kuma illa ga muhalli da wurin noma da hanyoyin ruwa da sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MUHALLINKA_RAYUWARKA_2026-08-15_NASIRU.mp3?guid=c0674bc6-98da-11f1-8b5c-9f95149eb222&source=GJlXzGgqHj)

## [Waiwaye game da muhimman labarai da suka faru a wannan makon](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260815-waiwaye-game-da-muhimman-labarai-da-suka-faru-a-makon?GJlXzGgqHj)

_2026-08-15 · Mu Zagaya Duniya_

A Colombia, wata girgizar ƙasa mai karfin maki 7.4 da ta afkawa ƙasar da ke kudancin Amurka tare da hallaka akalla mutane sama da 100, yayin da wasu da dama suka jikkata,a cikin shirin da ke waiwaye game da muhimman abubuwan da suka faru a makon da mu kayi ban kwana,wato Mu zagaya Duniya za ku ji irin wainar da aka tuya a wasu ƙasashe..............

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/FOCUS-15-08-2026-OUMAROU.mp3?guid=2b9aa3dc-9874-11f1-b79d-572f06304149&source=GJlXzGgqHj)

## [Cigaban kasuwar hannayen jari na nufin rayuwa ta fara inganta ga talakan Najeriya?](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260812-cigaban-kasuwar-hannayen-jari-na-nufin-rayuwa-ta-fara-inganta-ga-talakan-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-08-12 · Kasuwanci_

A ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026, mujalar Bloomberg da ke bibiyar harkokin tattalin arzikin ƙasashen duniya, ta bayyana kasuwar hannayen jarin Najeriya a matsayin ta ɗaya a duniya a fannin dala, wajen yi wa ta Koriya ta Kudu fintinƙau. Masana tattalin arziki sun alakanta wannan gagarumin ci gaba da kasuwar ta samu da sauye-sauye masu tsauri da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-ECO-NIGERIA_STOCK_01-2026-08-12-ABBA.mp3?guid=97590ebc-962e-11f1-b899-f3a546cf71d4&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda cutar kwalara ta jefa ɗumbin mutane cikin firgici a jihar Bornon Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260810-yadda-cutar-kwalara-ta-jefa-%C9%97umbin-mutane-cikin-firgici-a-jihar-bornon-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-08-10 · Lafiya Jari ce_

A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan sake ɓarkewar cutar kwalara ko kuma amai da gudawa a jihar Borno, lamarin da ya jefa ɗimbin jama’a a yanayi na matuƙar damuwa damuwa musamman bayan da rahotanni ke cewa an samu yaɗuwar annobar cutar har a yankunan da ake ajje da ɗimbin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_HEALTH_CHOLERA_OUTBREAK-BORNO_2026-08-10_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=1fb14004-94a4-11f1-8a45-d3a42fe1dd18&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalli](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260808-yadda-dazuka-ke-taimakawa-wajan-kare-muhalli-1?GJlXzGgqHj)

_2026-08-08 · Muhallinka Rayuwarka_

Shirin Muhallinka rayuwarka na wannnan mako tare da Nasiru Sani ya duba irin gudun mawar da ganzun daji ke bayarwa wajan kare muhalli daga matsalar sauyin yanayi Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_ENVIRONMENT_2026-08-08_NASIRU.mp3?guid=8439a122-936b-11f1-9f3b-976cfcc5ee76&source=GJlXzGgqHj)

## [Saudiya, Pakistan da Turkiya sun sanar da kulla yarjejeniyar tsaro](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260808-saudiya-pakistan-da-turkiya-sun-sanar-da-kulla-yarjejeniyar-tsaro?GJlXzGgqHj)

_2026-08-08 · Mu Zagaya Duniya_

Ƙasashen Saudiya,Pakistan da kuma Turkiya sun sanar da kulla yarjejeniyar tsaro a tsakanin su yau juma’a a birnin Djeddah a wani yanayi da ake kara samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya. Yarjejeniyar da aka raɗa wa suna yarjeniyar Makka, ko baya ga harakar tsaro ta kuma tanadi faɗaɗa alakar da ke tsakanin ƙasashen a fanoni daban-daban.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/FOCUS-MAG-08-08-2026-OUMAROU_OK.mp3?guid=1e167dc8-92f5-11f1-88e4-8b6f5a9a6888&source=GJlXzGgqHj)

## [Earn crypto for idle GPUs (Sponsored)](https://crawlproof.com/a/BCH5CmSWhkOg)

_2026-08-08 · **Sponsored**_

Run one CLI, host Qwen/Llama/Mistral, and earn BTC, ETH, SOL, or USDC

## [Ghana ta yiwa ƙasashen Afrika fintinkau a fannin ci gaban hada-hadar kuɗaɗe ta wayar hannu](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260805-ghana-ta-yiwa-%C6%99asashen-afrika-fintinkau-a-fannin-ci-gaban-hada-hadar-ku%C9%97a%C9%97e-ta-wayar-hannu?GJlXzGgqHj)

_2026-08-05 · Kasuwanci_

Shirin na wannan mako ya duba yadda Ƙasar Ghana ta zama jagaba a fannin hada\_hadar kuɗi ta wayar hannu a Afirka, inda a wannan shekara kaɗai kamfanonin sadarwar wayar tafi da gidanka suka yi hada-hadar sama da Cidi biliyan 40. Ku danna lamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-ECO-2026-08-05-ABBA.mp3?guid=20aeb190-90bb-11f1-a386-53b399c4dc05&source=GJlXzGgqHj)

## [Wane tasiri Chamfi ke da shi wajen gyarawa ko kuma ruguza aure musamman a zamanin baya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260804-wane-tasiri-chamfi-ke-da-shi-wajen-gyarawa-ko-kuma-ruguza-aure-musamman-a-zamanin-baya?GJlXzGgqHj)

_2026-08-04 · Al'adun Gargajiya_

Shirin Al'adunmu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan yadda Chamfe-Chamfe ke shafar lamuran auratayya musamman a zamanin baya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shrin tare da Abdullahi Isa

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_AL_ADU_CAMFE-CAMFE_2026-08-04.mp3?guid=1b70e28a-8ff2-11f1-9301-f76b6586dacb&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda cutar Bilharzia ko Tsagiya ke barazana ga rayuwar ɗimbin ƴan Afirka](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260803-yadda-cutar-bilharzia-ko-tsagiya-ke-barazana-ga-rayuwar-%C9%97imbin-%C6%B4an-afirka?GJlXzGgqHj)

_2026-08-03 · Lafiya Jari ce_

A wannan makon shirin na lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya yi duba duba kan cutar Schistosomiasis (shustosumayusus) ko Bilharzia koma Snail fever kamar yadda wasu ke kiranta, cutar nan dai da aka fi sani da tsagiya a hausance, cutar alƙaluma ke nuni da cewa kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da ita na a nahiyar Afrika. Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani.......

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_HEALTH-TSAGIYA-NIGER-2026-08-03-_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=2a3be68e-8f1b-11f1-bf58-db88ccb4d9a8&source=GJlXzGgqHj)

## [Matakan da manoman Nijar ke ɗauka a lokutan da aka fuskanci ƙarancin ruwan sama](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260802-matakan-da-manoman-nijar-ke-%C9%97auka-a-lokutan-da-aka-fuskanci-%C6%99arancin-ruwan-sama?GJlXzGgqHj)

_2026-08-02 · Muhallinka Rayuwarka_

A Jamhuriyar Nijar,manoman dai sun fara da taka tsan-tsan ne saboda tsila-tsillar saukar ruwan shukar da suke fuskanta da kuma yanda ake samun dogon lokaci kafin saukar wani ruwan bayan saukar na farko, abun dake sanya shukar da suka yi ta mutu a ɗan wani lokaci.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_ENVIRONMENT_2026-08-01_NASIRU.mp3?guid=cb449ef2-8e5f-11f1-a4c7-ff4828f50443&source=GJlXzGgqHj)

## [Mu Zagaya Duniya: Zafin alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta kudu](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260801-mu-zagaya-duniya-zafin-ala%C6%99a-tsakanin-najeriya-da-afrika-ta-kudu?GJlXzGgqHj)

_2026-08-01 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin "Mu Zagaya Duniya" tare da Oumarou Sani kamar kowanne mako ya taɓo muhimman labaran da suka faru a sassa daban daban na Najeriya ciki har da zafin alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu, kana dambarwar ma'aikatar Bogi a Najeriya sai kuma batun cika shekaru 3 da faro mulkin Soji a Najeriya sannan batun ficewar Chadi daga kotun ICC. Zamu soma shirin daga Najeriya inda batun kirkirar…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-FOCUS-2026-08-01.mp3?guid=484c507a-8d8e-11f1-818c-f56c7bb28b0a&source=GJlXzGgqHj)

## [Illar cushen kusan naira tiriliyan 1 a kasafin kuɗin Najeriya ga tattalin arziƙi](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260729-illar-cushen-kusan-naira-tiriliyan-1-a-kasafin-ku%C9%97in-najeriya-ga-tattalin-arzi%C6%99i?GJlXzGgqHj)

_2026-07-29 · Kasuwanci_

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, ya mayar da hankali ne kan yadda aka gano cushen kusan Naira triliyan ɗaya cikin kasafin kuɗin Najeriya na wannan shekarar ta 2026, domin sayen motocin alfarma da kuma ayyukan tallafa wa jama'a. Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoton da wata cibiyar da ke sa’ido kan yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗen kasafi a Najeriya wato Tracka. Cibiyar…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-ECO-NIGERIA-2026-07-29-ABBA.mp3?guid=c629a012-8b25-11f1-8c82-592ac6ceb892&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda ba a samun sabbin ƙasashen da ke lashe Gasar Kofin Duniya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/wasanni/20260727-yadda-ba-a-samun-sabbin-%C6%99asashen-da-ke-lashe-gasar-kofin-duniya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-27 · Wasanni_

Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda ba a samun sabbin ƙasashen da ke lashe gasar kofin duniya. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-SPORTS-2026-07-27-KHAMIS.mp3?guid=98f50f0c-8993-11f1-ba7c-9f6e96b6eca3&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda farashin magunguna ke tashi a lokacin damuna da aka fi fama da cutuka](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260727-yadda-farashin-magunguna-ke-tashi-a-lokacin-damuna-da-aka-fi-fama-da-cutuka?GJlXzGgqHj)

_2026-07-27 · Lafiya Jari ce_

Shirin Lafiya Jari ce na wannan mako ya yi dubi ne kan yawaitar cututtuka a irin wannan lokaci na damuna, daidai lokacin da bayanai ke nuni da cewa farashin magunguna ya yi tashin gauron zabbi. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_HEALTH-PHARMACY-COST_2026-07-27_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=06dafbb8-8993-11f1-be6d-07d1b4f8dfb8&source=GJlXzGgqHj)

## [Illolin karancin gonaki kusa da jama'a da yadda ya shafi burin bunkasa samar da abinci](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260725-illolin-karancin-gonaki-kusa-da-jama-a-da-yadda-ya-shafi-burin-bunkasa-samar-da-abinci?GJlXzGgqHj)

_2026-07-25 · Muhallinka Rayuwarka_

Sau da dama, masu burin shiga harkokin noma a Nigeria kan canza tunaninsu, sakamakon rashin samun gonakin da za su noma kusa da gari, lamarin da kan tilasta su jingine aniyarsu ta yin noma. Gwamnatin Nigeria dai, ta sha kira ga ‘yan kasar da su koma gona, la’akari da yadda Allah ya albarkaci kasar da wadatattun filayen noma da kuma yanayi mai kyau da za a iya noma kowane irin nau’in kayan abinci.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/environ_saturd.mp3?guid=f7ae9224-885e-11f1-acb5-9f65143c79d8&source=GJlXzGgqHj)

## [Mu zagaya Duniya: Kotu ta yiwa ƴan ta'adda ɗaurin rai da rai a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260725-mu-zagaya-duniya-kotu-ta-yiwa-%C6%B4an-ta-adda-%C9%97aurin-rai-da-rai-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-25 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin Mu zagaya duniya tare da Oumarou Sani ya mayar da hankali kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin wanda ya taɓo dukkanin batutuwa kama da tsaro da tattalin arziƙi, siyasar ƙasashe dama rikice-rikice.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_FOCUS_OUMAROU.mp3?guid=3362853c-880a-11f1-9798-81f4c6a80390&source=GJlXzGgqHj)

## [100,000 Bonus Points Await You (Sponsored)](https://crawlproof.com/a/QNxaqn5eM5KG)

_2026-07-25 · **Sponsored**_

Earn 100,000 bonus points after spending $5,000 in the first 3 months.

## [Matakin matatar Ɗangote ya fusata ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260722-matakin-matatar-%C9%97angote-ya-fusata-%C6%99ungiyar-dillalan-man-fetur-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-22 · Kasuwanci_

Shirin a wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi dubi ne kan matakin da ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta sanar na dakatar da sayen mai daga matatar Dangote, sakamakon matakin da matatar ta ɗauka na fara sayar musu da man da take tacewa da dala maimakon Naira. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-ECO-2026-07-22-ABBA.mp3?guid=4d02caa6-85bc-11f1-b633-d112579d0824&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda gwamnatin Kano ta yi nasarar rage mace-macen mata a lokacin haihuwa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260720-yadda-gwamnatin-kano-ta-yi-nasarar-rage-mace-macen-mata-a-lokacin-haihuwa?GJlXzGgqHj)

_2026-07-20 · Lafiya Jari ce_

Shirin a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan nasarar da jihar Kano ke iƙirarin samu bayan fitar wani rahoto da ke cewa an samu raguwar mace-macen mata a lokacin haihuwa a sassan jihar wadda a baya ke sahun gaba wajen asarar rayukan ɗimbin mata a lokacin haihuwa ko goyon ciki Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin..........

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_HEALTH-MATERNAL_MORTALITY_2026-07-20_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=b4244128-8423-11f1-a592-7d8e98d13a62&source=GJlXzGgqHj)

## [Spain ta lashe kofin duniya karo na biyu a tarihi](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/wasanni/20260720-spain-ta-lashe-kofin-duniya-karo-na-biyu-a-tarihi?GJlXzGgqHj)

_2026-07-20 · Wasanni_

Shirin Duniyar wasanni a wannan makon tare da Khamis Saleh ya yi duba ne a gameda nasarar da tawagar Spain ta yi kan takwararta ta Argentina a gasar cin kofin duniya karo na 23 Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-SPORTS-W_CUP_FINAL-2026-07-20-KHAMIS.mp3?guid=1cb943be-841f-11f1-87a3-7d8e98d13a62&source=GJlXzGgqHj)

## [Ceto ɗalibai da malamansu a Oyo na cikin labarai da suka ja hankali a makon jiya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260718-ceto-%C9%97alibai-da-malamansu-a-oyo-na-cikin-labarai-da-suka-ja-hankali-a-makon-jiya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-18 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Oumar Sani ya yi bitar wasu daga cikin manyan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka yi bankwana da shi ciki har da nasarar kuɓutar da dalibai tare da malamansu 40 a jihar Oyo da ke Najeriya bayan sun shafe kwanaki 50 a hannun wadanda su kayi garkuwa dasu.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-FOCUS-2026-07-18-OUMAROU.mp3?guid=2b04eb7a-8290-11f1-a15b-7313728c1c34&source=GJlXzGgqHj)

## [Makomar ilimin yara a Kano na cikin halin rashin tabbas](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260714-makomar-ilimin-yara-a-kano-na-cikin-halin-rashin-tabbas?GJlXzGgqHj)

_2026-07-14 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin na wannan makon cigaba ne kan wanda muka gabatar a makon jiya, wanda ya gano yadda yara a wasu yankunan jihar Kano basa zuwa makaranta saboda yawon tallace-tallace domin tara kudin kayan ɗaki. Yayin da su kuma mazan suke diban yashi da fasa Dutse, da sunan wai su taso suna da sana'ar dogaro da kai. Yankunan da wannan lamari yafi kamari sun hada da Challawa, Kafin Maiyaki, Madobi, Gora, da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-SCI-AND-TECH-2026-07-14.mp3?guid=471fafce-7f62-11f1-a08a-45e43ba2eff1&source=GJlXzGgqHj)

## [Muhimmancin zurfafa bincike a dukkan fannoni gabanin aure](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260714-muhimmancin-zurfafa-bincike-a-dukkan-fannoni-gabnin-aure?GJlXzGgqHj)

_2026-07-14 · Al'adun Gargajiya_

Shirin 'Al'adunmu Na Gado zai yi duba ne kan muhimmancin zurfafa bincike gabanin aure. Al’adun al’ummar Hausawa da ma mafi yawan al’ummomin da ke zaune a yankin arewacin Nigeria, sun sahale wa iyaye, gudanar da bincike kan yaron da ya nuna kai yana son ‘yarsu da aure, kamar yadda shima bangaren angon, kan yi bincike kan yanayin lafiya, tarbiyya da nasabar yarinyar. Irin wannan bincike, ya taimaka…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_AL_ADU_-BICINKE_KAFIN_AURATAR_DA_YA_A_2026-07-14.mp3?guid=dacbce80-7f60-11f1-bf2b-1dab813a2f24&source=GJlXzGgqHj)

## [Matsalar ƙarin mahaifa ko fibroids ga lafiyar mata](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260713-matsalar-%C6%99arin-mahaifa-ko-fibroids-ga-lafiyar-mata?GJlXzGgqHj)

_2026-07-13 · Lafiya Jari ce_

Shirin Lafiya Jari Ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan cutar ƙaba ko ƙarin mahaifi ko kuma fibroids da ke addabar tarin mata ta yadda da dama ke rayuwa da shi ba tare da sani ba, yayinda wanzuwarsa a mahaifa kan haddasa matsala ga yanayin haihuwa ga matan. Galibi mata a tsakanin shekaru 35 zuwa 37 ne suka fi kamuwa da wannan lalura ta Fibroids, a wani yanayi da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_HEALTH-WOMEN_FIBROIDS-2026-07-13_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=90130864-7ea1-11f1-89b1-d560f093ee90&source=GJlXzGgqHj)

## [Sharhin yadda wasannin kwata final na gasar cin kofin duniya suka gudana](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/wasanni/20260713-sharhin-yadda-wasannin-kwata-final-na-gasar-cin-kofin-duniya-suka-gudana?GJlXzGgqHj)

_2026-07-13 · Wasanni_

Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali kan wasannin gab da na kusa da ƙarshe na gasar cin kofin duniya da aka kammala tsakanin ƙasashe 8 wanda kuma kawo yanzu ya rage ƙasashe 4 a wannan tafiya wadda ta faro da ƙasashe 48. A wasannin dai Faransa ta yi waje da Morocco yayinda Spain ta yi waje da Belgium kana Ingila ta yi waje da Norway yayinda Argentina mai…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-SPORTS-WORLD_CUP_4-2026-07-13-KHAMIS.mp3?guid=2b664fd0-7ea0-11f1-9353-1305093bc657&source=GJlXzGgqHj)

## [Faɗa ya sake ɓarkewa tsakanin Amurka da Iran bayan rugujewar yarjejeniya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260711-fa%C9%97a-ya-sake-%C9%93arkewa-tsakanin-amurka-da-iran-bayan-rugujewar-yarjejeniya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-11 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin a wannan makon zai leka Gabas ta Tsakiya inda rikici ya sake barkewa tsakanin Amurka da Iran abin da ya kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna ta watanni uku da suka cimma a tsakaninsu. Bayan nan, shirin zai taɓo wasu mahimman lammuran da suka wakana a sassan yammacin nahiyar Afirka, musamman Najeriya, Nijar da Kamaru.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/FOCUS-2026-07-11-OUMAROU.mp3?guid=ae77c4ce-7cef-11f1-ae5c-e1de21817b8b&source=GJlXzGgqHj)

## [Rashin rassan bankuna ya tilastawa al'ummar karkara rungumar POS a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260708-rashin-rassan-bankuna-ya-tilastawa-al-ummar-karkara-rungumar-pos-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-08 · Kasuwanci_

Shirin kasuwa akai miki dole dake bibiyar harkokin kasuwanci da tattalin arziki na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ci gabar fasahar zamani da aka samu a fannonin haɗar-haɗur ƙudi a Najeriya, ke shafar al’ummomi a yankunan ƙarƙara.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-ECO-2026-07-8-ABBA.mp3?guid=fcec10f0-7abb-11f1-8ee7-4bd5fac9b0c9&source=GJlXzGgqHj)

## [Marketplace for AI-Powered Professionals (Sponsored)](https://crawlproof.com/a/QGeDtZrqeOZs)

_2026-07-08 · **Sponsored**_

Find professionals who use ChatGPT, Copilot, and Claude to deliver work faster.

## [Yadda makomar ilimin yaran karkara a Najeriya ke cikin rashin tabbas](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260708-yadda-makomar-ilimin-yaran-karkara-a-najeriya-ke-cikin-rashin-tabbas?GJlXzGgqHj)

_2026-07-08 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A wannan makon, shirin ya nufi yankunan karkara, inda inda gine-ginen makarantu ke ci gaba da kasancewa a matsayin kango, kasancewar babu dalibai. A wasu wuraren kuma, azuzuwan sun zama fanko, yayin da matasa da yara suka ƙaurace wa shiga, ‘yan mata na fita birni yin tallace-tallace, su kuma samari na dambatawa da aikin ƙwadagon fasa duwatsu da ɗiban yashi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-SCI-AND-TECH-2026-07-07.mp3?guid=4df503e4-7abc-11f1-ad90-8115b569da94&source=GJlXzGgqHj)

## [Tawagogin ƙasashen Afirka 7da aka yi waje dasu bayan sun tsallaka zagayen ƴan 32](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/wasanni/20260706-tawagogin-%C6%99asashen-afirka-7da-aka-yi-waje-dasu-bayan-sun-tsallaka-zagayen-%C6%B4an-32?GJlXzGgqHj)

_2026-07-06 · Wasanni_

Bayan nasarar da tawagogin ƙasashen Afrika 9 suka yi na kaiwa zagayen ƴan 32 a gasar lashe kofin duniya, wani lamari da ya sanya nahiyar ta kafa tarihin samun yawan wakilai a wannan zagaye, sai dai kuma ana iya cewa murna ta koma ciki domin dai tuni aka yi waje da 7 daga cikin 9. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-SPORT-WORLD_CUP_4-2026-07-06-KHAMIS.mp3?guid=704faea0-7920-11f1-bba2-1502fde6b6ee&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda cutar Typhiod ke barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a Afirka da Asiya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260706-yadda-cutar-typhiod-ke-barazana-ga-rayuwar-miliyoyin-mutane-a-afirka-da-asiya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-06 · Lafiya Jari ce_

Shirin na Lafiya Jari ce zai a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan zazzaɓin Typhoid, cuta mai haɗari wadda ƙwayar cutar Salmonella Typhi ke haddasawa, inda ta kan yaɗu ta hanyar abinci ko ruwan da ya gurɓata. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_HEALTH-TYPHOID_FEVER-2026-07-06_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=fc6d962a-791d-11f1-9877-6d2c5b2cd760&source=GJlXzGgqHj)

## [Bitar muhimman labarun da suka faru a mako daga Rfi hausa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260704-bitar-muhimman-labarun-da-suka-faru-a-mako-daga-rfi-hausa?GJlXzGgqHj)

_2026-07-04 · Mu Zagaya Duniya_

Ƙungiyar kare hakin bil Adam Amnesty International ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu da gaza kare ƴan Najeriya daga matsalolin ta’addanci da na tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.........

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-FOCUS-2026-07-04-OUMAROU.mp3?guid=f190a064-7772-11f1-a2ec-b7ac14afbbef&source=GJlXzGgqHj)

## [Ana samun ƙaruwar cin bashin kuɗin kiran waya tsakanin jama'ar Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260701-ana-samun-%C6%99aruwar-cin-bashin-ku%C9%97in-kiran-waya-tsakanin-jama-ar-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-01 · Kasuwanci_

Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan Najeriya suka rungumi ɗaukar bashin kiran waya, wanda wani rahoto ya ce, a bara kaɗai anci bashin kiran waya da ƙudinsu ya kai Naira Tiriliyan 4 da biliyan 61. Wasu bayanai da cibiyar fintech firms Optasia mai tattara alƙaluman shige da ficen kuɗaɗen layukan sadarwa ta fitar a baya-bayan nan, ya…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-ECO-AIRTIME-2026-07-01-ABBA.mp3?guid=1d148780-752c-11f1-ab18-ad9b86483aa0&source=GJlXzGgqHj)

## [Makomar makarantun gwaji na harsunan gida a Jamhuriyar Nijar.](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260630-makomar-makarantun-gwaji-na-harsunan-gida-a-jamhuriyar-nijar?GJlXzGgqHj)

_2026-06-30 · Al'adun Gargajiya_

Shirin wannan makon zai duba makomar makarantun gwaji na harsuna gida da suka haɗa harshen Hausa. A waɗannan makarantu, za a riƙa koyarwa da harsunan gida. Za a koya wa yara sana'o'i irin na gargajiya, a kuma koya musu adabin harsshe da sauransu.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_TASIRIN_MAKARANTU_A_HARSHEN_HAUSA_2026-06-29.mp3?guid=d269c5d4-746c-11f1-8c22-432894e2c7a6&source=GJlXzGgqHj)

## [Taron ƙaddamar da littafin tarihi na wani fitaccen matashi a Kanon Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260630-taron-%C6%99addamar-da-littafin-tarihi-na-wani-fitaccen-matashi-a-jiha-kano?GJlXzGgqHj)

_2026-06-30 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan taron ƙaddamar da sabon littafin tarihin nan mai suna 'Mu San Magabata', wanda fitaccen matashin marubuci Kabiru Ahmad Kwalli ya rubuta da aka gudanar a jihar Kanon Najeriya. Taron ya haɗa masana, sarakuna, da ɗandazon al'umma domin duba yadda za a ceto tarihin ƙasar Hausa da ke shirin bacewa. Wannan littafi, kamar yadda masana da dama suka bayyana,…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SCI-AND-TECH-2026-06-30.mp3?guid=42c72b3a-746a-11f1-8632-8da6f2af1ad5&source=GJlXzGgqHj)

## [Ƙaruwar masu fama da cutar sikila a Jamhuriyar Kamaru](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/lafiya-jari-ce/20260629-%C6%99aruwar-masu-fama-da-cutar-sikila-a-jamhuriyar-kamaru?GJlXzGgqHj)

_2026-06-29 · Lafiya Jari ce_

A wannan makon shirin ya yi duba ne kan ƙaruwar masu fama da cutar sikila a jamhuriyyar Kamaru bayan fitar wani rahoto da ke cewa cikin shekara 1 kaɗai an tattara alƙaluman sabbin mutum dubu 6 da aka gano suna ɗauke da cutar. Wannan cuta mai alaƙa da nau’in jini, na daga cikin matakan yaƙi da ita shi ne tabbatar da gwaje-gwajen jini tun kafin aure don kaucewa haifar yara masu ɗauke da ita, ganin…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_HEALTH-CAMEROON-SICKLE_CELL_2026-06-29_AZIMA_BASHIR_AMINU.mp3?guid=9d2cbfb0-73aa-11f1-b4a2-0934dbde6202&source=GJlXzGgqHj)

## [Irin rawar da ƙasashen Afirka suka taka a gasar Kofin Duniya ta 2026](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/wasanni/20260629-irin-rawar-da-%C6%99asashen-afirka-suka-taka-a-gasar-kofin-duniya-ta-2026?GJlXzGgqHj)

_2026-06-29 · Wasanni_

Shirin a wannan lokaci zayyi duba ne kan yadda irin rawar da ƙasashen Afrika suka taka a wasannin rukuni a gasar lashe kofin duniya. A ƙarshen mako ne dai aka kammala wasanni rukuni, abinda ke nuna cewar an buga wasanni 72 daga cikin 104 da za a yi a wannan gasa. Sakamakon waɗannan wasani da aka yi ya nuna cewar anyi waje da tawagogin ƙasashe 16 daga cikin 48 dake fafatawa a gasar, inda ƙasashe 32…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SPORTS-WORLD_CUP_GROUP-2026-06-29-KHAMIS.mp3?guid=f8f32f42-73a9-11f1-a489-09e3c4700f92&source=GJlXzGgqHj)

## [Ana ci gaba da laluben dubban mutanen da suka ɓata a girgizar kasa a Venezuela](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260627-ana-ci-gaba-da-laluben-dubban-mutanen-da-suka-%C9%93ata-a-girgizar-kasa-a-venezuela?GJlXzGgqHj)

_2026-06-27 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin na wannan mako zai soma ne daga Venezuela inda a yammacin ranar laraba girgiza ƙasa mai karfin maki 7 a ma’aunin celcius ta afkawa arewa maso yammacin ƙasar abin da ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali da alhini sakamakon rasa rayuka da dukiyoyi. Alkaluman hukumomi sun ce sama da mutum 900 ne suka rasayukansu kawo yanzu yayin da sama da 4,000 suka jikkata bayaga sama da 50,000 da suka yi…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-FOCUS-2026-06-27-OUMAROU.mp3?guid=68e1ffc6-7207-11f1-b8f3-294b7082853b&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda Hausawa ke cin kasuwar abincin gargajiya a Saudiyya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260623-yadda-hausawa-ke-cin-kasuwar-abincin-gargajiya-a-saudiyya?GJlXzGgqHj)

_2026-06-23 · Al'adun Gargajiya_

Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoullaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda Hausawa ke ɗabbaƙa al'adunsu ta hanyar hada-hadar abincin gargajiya a ƙasa mai tsarki ko kuma Saudi Arabiya. Kamar yadda ya ke sanannen abu, Hausawa kan rungumi mabanbantan sabbin al'adu amma yana matuƙar wahala a garesu su yi watsi da abincin da suturarsu, wannan ya sanya samun kasuwannin abincin gargajiya da dama…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_HAUSA_ALIMENTATION_IN_SDAUDIYYA-AL_ADU_2026-06-23_wav.mp3?guid=aab766be-6ef3-11f1-b228-7df663847292&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda aka gudanar da taron manyan masana na duniya a birnin Lagos](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260623-yadda-aka-gudanar-da-taron-manyan-masana-na-duniya-a-birnin-lagos?GJlXzGgqHj)

_2026-06-23 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A wannan makon, shirin ya mayar da hankali ne kan babban taron ƙungiyar Lagos Studies Association karo na goma da aka kammala a ƙarshen mako, wanda ya saba haɗa masana, malaman jami'o'i, da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje domin tattauna halin da ilimi yake ciki a nahiyar Afirka cikin wannan ƙarni. Wannan taro, wanda aka kafa shi shekaru goma da suka gabata a birnin…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SCI-AND-TECH-2026-06-23.mp3?guid=0bed7bfe-6ee4-11f1-b94e-ed9400012577&source=GJlXzGgqHj)

## [Muhimman abubuwan da suka faru a Gasar lashe Kofin Duniya kawo yanzu](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/wasanni/20260622-muhimman-abubuwan-da-suka-faru-a-gasar-lashe-kofin-duniya-kawo-yanzu?GJlXzGgqHj)

_2026-06-22 · Wasanni_

Shirin a wannan mako zai yi duba ne kan wasu muhimman abubuwan da suka faru a gasar lashe kofin duniya ciki har da karawar da Cote d’Ivoire ta sha kashi a hannun Jamus. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SPORTS_WORLD_CUP-2026-06-22-KHAMIS.mp3?guid=7fc2864a-6e0e-11f1-b942-055a56631484&source=GJlXzGgqHj)

## [Matsalar ambaliyar ruwa da kan dagula lamuran al’uma a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260620-matsalar-ambaliyar-ruwa-da-kan-dagula-lamuran-al-uma-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-06-20 · Muhallinka Rayuwarka_

Kamar kowace shekara, a bana ma ana hasashen samun ambaliyar ruwa a wasu ƙasashen yammacin Afrika, inda akan samu rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa. A Najeriya, an sha samun hasarar rayuka a sanadin matsalar ambaliyar ruwan, da kan rutsa da wasu yankunan ƙasar.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_ENVIRONMENT_2026-06-20_NASIR.mp3?guid=15ab0c30-6cda-11f1-b3a8-87bcfc211ad9&source=GJlXzGgqHj)

## [Shirin yayi bita kan harin da aka kai filin jirgin saman Yamai da ma wasu labarai](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260620-yadda-%C6%B4an-ta-adda-suka-farwa-babban-filin-sauka-da-tashin-jiragen-sama-na-birnin-yamai?GJlXzGgqHj)

_2026-06-20 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin na wannan mako ya mayar da hankali kan bitar muhimman labaran da suka faru a sassan duniya cikin makon da muke bankwana da shi. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sanni.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-FOCUS-20-06-2026-OUMAROU.mp3?guid=7c71a24c-6c8c-11f1-af21-e1ecc1e14ae7&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda tattalin arzikin Ghana ke haɓɓaka sannu a hankali](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/kasuwanci/20260617-yadda-tattalin-arzikin-ghana-ke-ha%C9%93%C9%93aka-sannu-a-hankali?GJlXzGgqHj)

_2026-06-17 · Kasuwanci_

Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane yadda tattalin arzikin ƙasar Ghana ke ci gaba da ɓunƙasa sannu a hankali. Ku danna alamar sauraro domin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-ECO-GHANA-2026-06-17-ABBA.mp3?guid=1b9f86f8-6a27-11f1-a907-5565451e5dd3&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda kiɗan Gurmi ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260616-yadda-ki%C9%97an-gurmi-ke-neman-%C9%93acewa-a-%C6%99asar-hausa?GJlXzGgqHj)

_2026-06-16 · Al'adun Gargajiya_

Shirinmu na yau ya leƙa sassan arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da duba yadda wani fitaccen kiɗan gargajiya, wato kiɗan Gurmi, ke fuskantar barazanar bacewa a fadin ƙasar Hausa. Shin me ke janyo haka, kuma wane canji fasahar zamani ta kawo? Gurmi, kayan kiɗa ne da aka sani tun kaka da kakanni, wanda ƙera ta hanyar amfani da ƙoƙon ƙwarya da aka rufe shi da fatar dabba, musamman fatar…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_AL_ADU_GURMI-_2026-06-16__EDITED.mp3?guid=a609a4dc-6963-11f1-883b-2962102ed5b9&source=GJlXzGgqHj)

## [Dalilan da ya sa ƴan Afirka suka juyawa tawagar Afirka ta Kudu baya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/wasanni/20260615-dalilan-da-ya-sa-%C6%B4an-afirka-suka-juyawa-tawagar-afirka-ta-kudu-baya?GJlXzGgqHj)

_2026-06-15 · Wasanni_

Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako tare da Khamis Saleh ya yi duba kan irin wainar da ake toyawa a gasar nema cin kofin duniya da ƙasashen Canada da Mexico da kuma Amurka ke karbar bakunci. Danna alamar sauti don sauraron cikakken shiri........

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SPORTS_WORLD_CUP_1-2026-06-15-KHAMIS.mp3?guid=dac0b758-6894-11f1-9caf-6381d4b04196&source=GJlXzGgqHj)

## [Masana na ci gaba da tsoratar da al'umma game da illolin da ke tattare da gurɓatacciyar iska](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/muhallinka-rayuwarka/20260613-masana-na-ci-gaba-da-tsoratar-da-al-umma-game-da-illolin-da-ke-tattare-da-gur%C9%93atacciyar-iska?GJlXzGgqHj)

_2026-06-13 · Muhallinka Rayuwarka_

A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan tasirin gurɓatacciyar iska ga lafiyar halittu da muhalli wato air pollution a turance. Iska na gurɓa ta ne ta hanyoyi da dama, kama daga hayaƙin na’urori wato injina a masana'antu, zuwa tarkacen bola ko kuma ƙone wasu abubuwa, wanda su ke kawo cikas ga yanayin muhalli tare kuma da kawo tazgaro ga lafiyar ɗan Adam.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_ENVIRONMENT_2026-06-13_NASIRU.mp3?guid=72bf283c-675f-11f1-80b2-415b24a3f3ce&source=GJlXzGgqHj)

## [Shirin ya fara da yadda aka buɗe bikin gasar cin kofin duniya a ƙasar Mexico](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260613-shirin-ya-fara-da-yadda-aka-bu%C9%97e-bikin-gasar-cin-kofin-duniya-a-%C6%99asar-mexico?GJlXzGgqHj)

_2026-06-13 · Mu Zagaya Duniya_

Ranar Alhamis 11 ga wannan watan aka yi bikin buɗe gasar cin kofin duniya karo na 23, gasar da itace karo na farko da ƙasashe 3, Amurka da Canada da kuma Mexico su ka karbi baƙunci, sai dai kuma an gudanar da zanga-zanga a wasu sassa na birnin ƙasar. Ƙasashe 48 ne ke fafata domin samun zakaran bana kuma yan wasa 1,248 da alkalan wasa 52 za su jagoranci wasanni 104 da za'a kwashe kwanaki 39 ana yi.…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/FOCUS-MAG-2026-06-13_OUMAROU.mp3?guid=fa4e6d9a-670e-11f1-8d8c-6d95a40a5b85&source=GJlXzGgqHj)

