# mako (audio feeds) — RSS Amplifier

Recent posts from the 5 feeds in the RSS Amplifier directory that cover mako.

Page: <https://rssamplifier.com/topics/mako/audio>  
Feed: <https://rssamplifier.com/topics/mako/audio.md>

---

## [Mu zagaya Duniya: Fara yaƙin neman zaɓe da musayar yawu tsakanin Tinubu da Atiku](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260822-mu-zagaya-duniya-fara-ya%C6%99in-neman-za%C9%93e-da-musayar-yawu-tsakanin-tinubu-da-atiku?GJlXzGgqHj)

_2026-08-22 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin ''Mu Zagaya Duniya" tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako kamar yadda aka saba ya taɓo muhimman batutuwan da suka faru a makon da muke bankwana da shi a Najeriya da sauran ƙasashen Afrika da ma duniya baki ɗaya. Cikin batutuwan da shirin ya taɓo akwai yakin neman zaben Najeriya, inda aka jiyo tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar na shan alwashin dawo da tallafin man fetur, da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/fakwas_22.mp3?guid=b1d8d4ba-9e13-11f1-a0ef-2f8168331588&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda matasa suka ƙera jirgi maras matuƙi mai cin Kilomita 30 a Kano](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260818-yadda-matasa-suka-%C6%99era-jirgin-maras-matu%C6%99i-mai-cin-kilomita-30-a-kano?GJlXzGgqHj)

_2026-08-18 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin a wannan makon ya leka Kanon Najeriya, inda aka gano wani sabon tarihin bunkasar kimiyya da fasaha da matasan yankin ke jagoranta. Wannan gagarumar bajinta dai wani matashi Abubakar Waiya, wanda ya daɗe yana fafutukar kera na'urorin shawagi ne ya ƙera jirgi maras matuƙi domin taimakawa ɓangaren tsaro da kuma boma. Jirgin da ya kera a yanzu yana da ikon tashi da kansa har na tsawon kilomita…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-SCI-AND-TECH-2026-08-18.mp3?guid=206ebca2-9ade-11f1-9d85-d5a741bcbce0&source=GJlXzGgqHj)

## [Halin da ake ciki game da al'adar 'Yan Kama da ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260818-halin-da-ake-ciki-game-da-al-adar-yan-kama-da-ke-neman-%C9%93acewa-a-%C6%99asar-hausa?GJlXzGgqHj)

_2026-08-18 · Al'adun Gargajiya_

Shirin "Al’adunmu na gado, ya mayar da hankali kan fadi-tashin da ake yi don adana tsohuwar al'adar mawaƙan 'Yan Kama a ƙasar Hausa. Waƙoƙin 'Yan Kama salon fasaha ne na musamman da mawaƙan ke amfani da shi domin nishaɗantarwa, inda suke sauya shahararrun waƙoƙi su koma na maganar abinci ko cika tumbi. A cikin shirin, masana sun bayyana yadda waɗannan mawaƙa ke da ƙwarewa wajen sarrafa harshen…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-CULTURE-YAN_KAMA-NURA-2026-08-18.mp3?guid=3edc0f5e-9ada-11f1-bce7-676e6058c92c&source=GJlXzGgqHj)

## [Waiwaye game da muhimman labarai da suka faru a wannan makon](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260815-waiwaye-game-da-muhimman-labarai-da-suka-faru-a-makon?GJlXzGgqHj)

_2026-08-15 · Mu Zagaya Duniya_

A Colombia, wata girgizar ƙasa mai karfin maki 7.4 da ta afkawa ƙasar da ke kudancin Amurka tare da hallaka akalla mutane sama da 100, yayin da wasu da dama suka jikkata,a cikin shirin da ke waiwaye game da muhimman abubuwan da suka faru a makon da mu kayi ban kwana,wato Mu zagaya Duniya za ku ji irin wainar da aka tuya a wasu ƙasashe..............

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/FOCUS-15-08-2026-OUMAROU.mp3?guid=2b9aa3dc-9874-11f1-b79d-572f06304149&source=GJlXzGgqHj)

## [Saudiya, Pakistan da Turkiya sun sanar da kulla yarjejeniyar tsaro](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260808-saudiya-pakistan-da-turkiya-sun-sanar-da-kulla-yarjejeniyar-tsaro?GJlXzGgqHj)

_2026-08-08 · Mu Zagaya Duniya_

Ƙasashen Saudiya,Pakistan da kuma Turkiya sun sanar da kulla yarjejeniyar tsaro a tsakanin su yau juma’a a birnin Djeddah a wani yanayi da ake kara samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya. Yarjejeniyar da aka raɗa wa suna yarjeniyar Makka, ko baya ga harakar tsaro ta kuma tanadi faɗaɗa alakar da ke tsakanin ƙasashen a fanoni daban-daban.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/FOCUS-MAG-08-08-2026-OUMAROU_OK.mp3?guid=1e167dc8-92f5-11f1-88e4-8b6f5a9a6888&source=GJlXzGgqHj)

## [Wane tasiri Chamfi ke da shi wajen gyarawa ko kuma ruguza aure musamman a zamanin baya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260804-wane-tasiri-chamfi-ke-da-shi-wajen-gyarawa-ko-kuma-ruguza-aure-musamman-a-zamanin-baya?GJlXzGgqHj)

_2026-08-04 · Al'adun Gargajiya_

Shirin Al'adunmu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan yadda Chamfe-Chamfe ke shafar lamuran auratayya musamman a zamanin baya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shrin tare da Abdullahi Isa

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG_AL_ADU_CAMFE-CAMFE_2026-08-04.mp3?guid=1b70e28a-8ff2-11f1-9301-f76b6586dacb&source=GJlXzGgqHj)

## [Mu Zagaya Duniya: Zafin alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta kudu](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260801-mu-zagaya-duniya-zafin-ala%C6%99a-tsakanin-najeriya-da-afrika-ta-kudu?GJlXzGgqHj)

_2026-08-01 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin "Mu Zagaya Duniya" tare da Oumarou Sani kamar kowanne mako ya taɓo muhimman labaran da suka faru a sassa daban daban na Najeriya ciki har da zafin alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu, kana dambarwar ma'aikatar Bogi a Najeriya sai kuma batun cika shekaru 3 da faro mulkin Soji a Najeriya sannan batun ficewar Chadi daga kotun ICC. Zamu soma shirin daga Najeriya inda batun kirkirar…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-FOCUS-2026-08-01.mp3?guid=484c507a-8d8e-11f1-818c-f56c7bb28b0a&source=GJlXzGgqHj)

## [Mu zagaya Duniya: Kotu ta yiwa ƴan ta'adda ɗaurin rai da rai a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260725-mu-zagaya-duniya-kotu-ta-yiwa-%C6%B4an-ta-adda-%C9%97aurin-rai-da-rai-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-25 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin Mu zagaya duniya tare da Oumarou Sani ya mayar da hankali kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke bankwana da shi. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin wanda ya taɓo dukkanin batutuwa kama da tsaro da tattalin arziƙi, siyasar ƙasashe dama rikice-rikice.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_FOCUS_OUMAROU.mp3?guid=3362853c-880a-11f1-9798-81f4c6a80390&source=GJlXzGgqHj)

## [Savage FINcast &#8211; Episode 140: Dragon Two-in-One](https://fincast.guttertrash.net/savage-fincast-episode-140-dragon-two-in-one/)

_2026-07-24 · Jim · Savage Fincast_

After a long delay the Savage FINcast finally returns with double packed double reviews of Savage Dragon 279 and 280. Jim is joined by guest hosts, and Super Freaks contributors, Ken Albery (Savage She-Newt) and Simon Mallette St-Pierre (Average Dragon) to tackle the final solo-Dragon kid story, and the triumphant return of our title heroes … Continue reading

[Listen](https://media.blubrry.com/fincast/fincast.guttertrash.net/show/SavageFincastEpisode140.mp3)

## [Ceto ɗalibai da malamansu a Oyo na cikin labarai da suka ja hankali a makon jiya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260718-ceto-%C9%97alibai-da-malamansu-a-oyo-na-cikin-labarai-da-suka-ja-hankali-a-makon-jiya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-18 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Oumar Sani ya yi bitar wasu daga cikin manyan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka yi bankwana da shi ciki har da nasarar kuɓutar da dalibai tare da malamansu 40 a jihar Oyo da ke Najeriya bayan sun shafe kwanaki 50 a hannun wadanda su kayi garkuwa dasu.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-FOCUS-2026-07-18-OUMAROU.mp3?guid=2b04eb7a-8290-11f1-a15b-7313728c1c34&source=GJlXzGgqHj)

## [Stocks ranked by what execs say (Sponsored)](https://crawlproof.com/a/WJFhIf1LzUeR)

_2026-07-18 · **Sponsored**_

Evidence-backed watchlists from earnings calls and filings, cited to real transcripts—not guesses.

## [Makomar ilimin yara a Kano na cikin halin rashin tabbas](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260714-makomar-ilimin-yara-a-kano-na-cikin-halin-rashin-tabbas?GJlXzGgqHj)

_2026-07-14 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin na wannan makon cigaba ne kan wanda muka gabatar a makon jiya, wanda ya gano yadda yara a wasu yankunan jihar Kano basa zuwa makaranta saboda yawon tallace-tallace domin tara kudin kayan ɗaki. Yayin da su kuma mazan suke diban yashi da fasa Dutse, da sunan wai su taso suna da sana'ar dogaro da kai. Yankunan da wannan lamari yafi kamari sun hada da Challawa, Kafin Maiyaki, Madobi, Gora, da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-SCI-AND-TECH-2026-07-14.mp3?guid=471fafce-7f62-11f1-a08a-45e43ba2eff1&source=GJlXzGgqHj)

## [Muhimmancin zurfafa bincike a dukkan fannoni gabanin aure](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260714-muhimmancin-zurfafa-bincike-a-dukkan-fannoni-gabnin-aure?GJlXzGgqHj)

_2026-07-14 · Al'adun Gargajiya_

Shirin 'Al'adunmu Na Gado zai yi duba ne kan muhimmancin zurfafa bincike gabanin aure. Al’adun al’ummar Hausawa da ma mafi yawan al’ummomin da ke zaune a yankin arewacin Nigeria, sun sahale wa iyaye, gudanar da bincike kan yaron da ya nuna kai yana son ‘yarsu da aure, kamar yadda shima bangaren angon, kan yi bincike kan yanayin lafiya, tarbiyya da nasabar yarinyar. Irin wannan bincike, ya taimaka…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG_AL_ADU_-BICINKE_KAFIN_AURATAR_DA_YA_A_2026-07-14.mp3?guid=dacbce80-7f60-11f1-bf2b-1dab813a2f24&source=GJlXzGgqHj)

## [Faɗa ya sake ɓarkewa tsakanin Amurka da Iran bayan rugujewar yarjejeniya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260711-fa%C9%97a-ya-sake-%C9%93arkewa-tsakanin-amurka-da-iran-bayan-rugujewar-yarjejeniya?GJlXzGgqHj)

_2026-07-11 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin a wannan makon zai leka Gabas ta Tsakiya inda rikici ya sake barkewa tsakanin Amurka da Iran abin da ya kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna ta watanni uku da suka cimma a tsakaninsu. Bayan nan, shirin zai taɓo wasu mahimman lammuran da suka wakana a sassan yammacin nahiyar Afirka, musamman Najeriya, Nijar da Kamaru.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/FOCUS-2026-07-11-OUMAROU.mp3?guid=ae77c4ce-7cef-11f1-ae5c-e1de21817b8b&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda makomar ilimin yaran karkara a Najeriya ke cikin rashin tabbas](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260708-yadda-makomar-ilimin-yaran-karkara-a-najeriya-ke-cikin-rashin-tabbas?GJlXzGgqHj)

_2026-07-08 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A wannan makon, shirin ya nufi yankunan karkara, inda inda gine-ginen makarantu ke ci gaba da kasancewa a matsayin kango, kasancewar babu dalibai. A wasu wuraren kuma, azuzuwan sun zama fanko, yayin da matasa da yara suka ƙaurace wa shiga, ‘yan mata na fita birni yin tallace-tallace, su kuma samari na dambatawa da aikin ƙwadagon fasa duwatsu da ɗiban yashi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-SCI-AND-TECH-2026-07-07.mp3?guid=4df503e4-7abc-11f1-ad90-8115b569da94&source=GJlXzGgqHj)

## [Bitar muhimman labarun da suka faru a mako daga Rfi hausa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260704-bitar-muhimman-labarun-da-suka-faru-a-mako-daga-rfi-hausa?GJlXzGgqHj)

_2026-07-04 · Mu Zagaya Duniya_

Ƙungiyar kare hakin bil Adam Amnesty International ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu da gaza kare ƴan Najeriya daga matsalolin ta’addanci da na tattalin arziki da ake fama da shi a Najeriya.........

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-FOCUS-2026-07-04-OUMAROU.mp3?guid=f190a064-7772-11f1-a2ec-b7ac14afbbef&source=GJlXzGgqHj)

## [Makomar makarantun gwaji na harsunan gida a Jamhuriyar Nijar.](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260630-makomar-makarantun-gwaji-na-harsunan-gida-a-jamhuriyar-nijar?GJlXzGgqHj)

_2026-06-30 · Al'adun Gargajiya_

Shirin wannan makon zai duba makomar makarantun gwaji na harsuna gida da suka haɗa harshen Hausa. A waɗannan makarantu, za a riƙa koyarwa da harsunan gida. Za a koya wa yara sana'o'i irin na gargajiya, a kuma koya musu adabin harsshe da sauransu.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_TASIRIN_MAKARANTU_A_HARSHEN_HAUSA_2026-06-29.mp3?guid=d269c5d4-746c-11f1-8c22-432894e2c7a6&source=GJlXzGgqHj)

## [Taron ƙaddamar da littafin tarihi na wani fitaccen matashi a Kanon Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260630-taron-%C6%99addamar-da-littafin-tarihi-na-wani-fitaccen-matashi-a-jiha-kano?GJlXzGgqHj)

_2026-06-30 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan taron ƙaddamar da sabon littafin tarihin nan mai suna 'Mu San Magabata', wanda fitaccen matashin marubuci Kabiru Ahmad Kwalli ya rubuta da aka gudanar a jihar Kanon Najeriya. Taron ya haɗa masana, sarakuna, da ɗandazon al'umma domin duba yadda za a ceto tarihin ƙasar Hausa da ke shirin bacewa. Wannan littafi, kamar yadda masana da dama suka bayyana,…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SCI-AND-TECH-2026-06-30.mp3?guid=42c72b3a-746a-11f1-8632-8da6f2af1ad5&source=GJlXzGgqHj)

## [Ana ci gaba da laluben dubban mutanen da suka ɓata a girgizar kasa a Venezuela](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260627-ana-ci-gaba-da-laluben-dubban-mutanen-da-suka-%C9%93ata-a-girgizar-kasa-a-venezuela?GJlXzGgqHj)

_2026-06-27 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin na wannan mako zai soma ne daga Venezuela inda a yammacin ranar laraba girgiza ƙasa mai karfin maki 7 a ma’aunin celcius ta afkawa arewa maso yammacin ƙasar abin da ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali da alhini sakamakon rasa rayuka da dukiyoyi. Alkaluman hukumomi sun ce sama da mutum 900 ne suka rasayukansu kawo yanzu yayin da sama da 4,000 suka jikkata bayaga sama da 50,000 da suka yi…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-FOCUS-2026-06-27-OUMAROU.mp3?guid=68e1ffc6-7207-11f1-b8f3-294b7082853b&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda Hausawa ke cin kasuwar abincin gargajiya a Saudiyya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260623-yadda-hausawa-ke-cin-kasuwar-abincin-gargajiya-a-saudiyya?GJlXzGgqHj)

_2026-06-23 · Al'adun Gargajiya_

Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoullaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda Hausawa ke ɗabbaƙa al'adunsu ta hanyar hada-hadar abincin gargajiya a ƙasa mai tsarki ko kuma Saudi Arabiya. Kamar yadda ya ke sanannen abu, Hausawa kan rungumi mabanbantan sabbin al'adu amma yana matuƙar wahala a garesu su yi watsi da abincin da suturarsu, wannan ya sanya samun kasuwannin abincin gargajiya da dama…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_HAUSA_ALIMENTATION_IN_SDAUDIYYA-AL_ADU_2026-06-23_wav.mp3?guid=aab766be-6ef3-11f1-b228-7df663847292&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda aka gudanar da taron manyan masana na duniya a birnin Lagos](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260623-yadda-aka-gudanar-da-taron-manyan-masana-na-duniya-a-birnin-lagos?GJlXzGgqHj)

_2026-06-23 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A wannan makon, shirin ya mayar da hankali ne kan babban taron ƙungiyar Lagos Studies Association karo na goma da aka kammala a ƙarshen mako, wanda ya saba haɗa masana, malaman jami'o'i, da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje domin tattauna halin da ilimi yake ciki a nahiyar Afirka cikin wannan ƙarni. Wannan taro, wanda aka kafa shi shekaru goma da suka gabata a birnin…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SCI-AND-TECH-2026-06-23.mp3?guid=0bed7bfe-6ee4-11f1-b94e-ed9400012577&source=GJlXzGgqHj)

## [Dissecting Series A Rounds (Sponsored)](https://crawlproof.com/a/rtoqONlSUnZv)

_2026-06-23 · **Sponsored**_

Two real Series A cases: timelines, investor sequencing, and common founder mistakes.

## [Shirin yayi bita kan harin da aka kai filin jirgin saman Yamai da ma wasu labarai](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260620-yadda-%C6%B4an-ta-adda-suka-farwa-babban-filin-sauka-da-tashin-jiragen-sama-na-birnin-yamai?GJlXzGgqHj)

_2026-06-20 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin na wannan mako ya mayar da hankali kan bitar muhimman labaran da suka faru a sassan duniya cikin makon da muke bankwana da shi. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sanni.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-FOCUS-20-06-2026-OUMAROU.mp3?guid=7c71a24c-6c8c-11f1-af21-e1ecc1e14ae7&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda kiɗan Gurmi ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260616-yadda-ki%C9%97an-gurmi-ke-neman-%C9%93acewa-a-%C6%99asar-hausa?GJlXzGgqHj)

_2026-06-16 · Al'adun Gargajiya_

Shirinmu na yau ya leƙa sassan arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da duba yadda wani fitaccen kiɗan gargajiya, wato kiɗan Gurmi, ke fuskantar barazanar bacewa a fadin ƙasar Hausa. Shin me ke janyo haka, kuma wane canji fasahar zamani ta kawo? Gurmi, kayan kiɗa ne da aka sani tun kaka da kakanni, wanda ƙera ta hanyar amfani da ƙoƙon ƙwarya da aka rufe shi da fatar dabba, musamman fatar…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_AL_ADU_GURMI-_2026-06-16__EDITED.mp3?guid=a609a4dc-6963-11f1-883b-2962102ed5b9&source=GJlXzGgqHj)

## [Shirin ya fara da yadda aka buɗe bikin gasar cin kofin duniya a ƙasar Mexico](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260613-shirin-ya-fara-da-yadda-aka-bu%C9%97e-bikin-gasar-cin-kofin-duniya-a-%C6%99asar-mexico?GJlXzGgqHj)

_2026-06-13 · Mu Zagaya Duniya_

Ranar Alhamis 11 ga wannan watan aka yi bikin buɗe gasar cin kofin duniya karo na 23, gasar da itace karo na farko da ƙasashe 3, Amurka da Canada da kuma Mexico su ka karbi baƙunci, sai dai kuma an gudanar da zanga-zanga a wasu sassa na birnin ƙasar. Ƙasashe 48 ne ke fafata domin samun zakaran bana kuma yan wasa 1,248 da alkalan wasa 52 za su jagoranci wasanni 104 da za'a kwashe kwanaki 39 ana yi.…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/FOCUS-MAG-2026-06-13_OUMAROU.mp3?guid=fa4e6d9a-670e-11f1-8d8c-6d95a40a5b85&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da gagarumin taron sada zumunci](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260609-yadda-hausawa-mazauna-jamus-suka-gudanar-da-gagarumin-taron-sada-zumunci?GJlXzGgqHj)

_2026-06-09 · Al'adun Gargajiya_

Shirin Al'adun mu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da wani gagarumin taro. Ku danna alamar Saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG_AL_ADU_RANAR_HAUSA_A_JAMUS_2026-06-09.mp3?guid=8e023626-63df-11f1-a5a5-7be3d85db93d&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda talauci ke hana ɗalibai cikar burinsu](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260609-yadda-talauci-ke-hana-%C9%97alibai-cikar-burinsu?GJlXzGgqHj)

_2026-06-09 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi hasken rayuwa na wanna Mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsin tattalin arziki ke tilstawa ɗalibai haƙura da cikar burinsu na karatu, don kawai neman abin kaiwa baka, a kowacce rana. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsioyya Haruna.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-CI-AND-TECH-2026-06-09.mp3?guid=e91467ec-63de-11f1-afbf-7be3d85db93d&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda malaman makaranta suka gudanar da zanga-zanga kan rashin tsaro a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260606-yadda-malaman-makaranta-suka-gudanar-da-zanga-zanga-kan-rashin-tsaro-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-06-06 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin na wannan mako ya waiwaya halin da duniya ke ciki a fannin tsaro, rikice-rikice da kuma Diflomasiyya

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-FOCUS-2026-05-06-OUMAROU.mp3?guid=274a16a2-6190-11f1-b1ac-bb13b73344fd&source=GJlXzGgqHj)

## [Shirin kawar da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta na samun nasara a Jigawa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260602-shirin-mayar-da-yaran-da-ba-sa-zuwa-makaranta-ajujuwa-na-samun-kar%C9%93uwa-a-jihar-jigawa?GJlXzGgqHj)

_2026-06-02 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya sake waiwayar matsalar nan ce ta yawaitar yaran da ba za zuwa makaranta a arewacin Najeriya, batun da a fannin ilimi ke ci wa al’ummar yankin tuwo a ƙwarya. Masu iya magana dai na cewa ‘mai rai ba ya rasa motsi’ domin kuwa duk da girman da wannan matsala ta yi a Najeriya musamman ma yankin arewacin ƙasar, akwai waɗanda suka tashi tsaye wajen ganin sun…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SCI_AND_TECH-NURA-2026-01-02.mp3?guid=2de1bef4-5e69-11f1-8a60-7567fe6d1d99&source=GJlXzGgqHj)

## [Mahajjata kusan miliyan biyu sun gudanar da aikin Hajjin bana](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260530-mahajjata-kusan-miliyan-biyu-sun-gudanar-da-aikin-hajjin-bana?GJlXzGgqHj)

_2026-05-30 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Oumarou Sani, kamaar yadda aka saba ya yi bitar wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana. Daga cikin muhimman batutuwan kuma akwai, yadda Musulmi kusan miliyan biyu suka samu nasarar gudanar da aikin Hajjin bana. Shirin ya kuma leƙa Yankin Gabas ta Tsakiya domin jin halin da ake ciki, musamman kan ƙoƙarin kawo…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG-FOCUS-2026-05-30-OUMAROU.mp3?guid=5dbefd4a-5b98-11f1-946d-99203303f8e3&source=GJlXzGgqHj)

## [Gombe: Fulani sun yi taro kan warware matsalolin da ke ɓata musu suna](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260528-gombe-fulani-sun-yi-taro-kan-warware-matsalolin-da-ke-%C9%93ata-musu-suna?GJlXzGgqHj)

_2026-05-28 · Al'adun Gargajiya_

Shirin Al'adunmu na Gado a wannan mako, yayi tattaki ne zuwa garin Gombe, inda Al'ummar Fulani suka gudanar da wani taro na farfaɗo da Al'adunsu na Gargajiya, da kuma tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi wajen maido da Tarbiyya, gami da zamantakewa kyakkyawa a tsakanin Fulanin da kuma sauran Ƙabilu.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG_AL_ADU_2026-05-26.mp3?guid=ed37015a-5aaf-11f1-b034-0dd788dec897&source=GJlXzGgqHj)

## [RFI Hausa ta cika shekaru 19 da fara watsa labarai cikin harsshen Hausa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260523-rfi-hausa-ta-cika-shekaru-19-da-fara-watsa-labarai-cikin-harsshen-hausa?GJlXzGgqHj)

_2026-05-23 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya fara ne da labarin cikar wannan tasha ta RFI Hausa shekaru 19 da kafuwa. Ranar alhamis 21 ga wannan watan gidan Rediyonku na RFI sashen Hausa ya cika shekara daya- daya har 19 da soma yada shirye-shiryensa . A shekara 2007 ne kwarrariyar ƴar Jarida Lanni Smith ta kirkiri sashen Hausa na RFI da aka yi wa matsuguni a birnin Lagos da ke kudu maso yammacin Najeriya. Kuma…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/FOCUS-MAG-2026-05-23-OUMAROU.mp3?guid=a048d240-566f-11f1-9618-41a384e073d7&source=GJlXzGgqHj)

## [One Cloud, Every AI Layer (Sponsored)](https://crawlproof.com/a/OFDg7DVAkxct)

_2026-05-23 · **Sponsored**_

Run agents, inference, and infrastructure on one stack — economics improve as you scale.

## [Ɗimbin matasa na haƙura da karatun boko saboda rashin tabbas kan samun aiki](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260519-%C9%97imbin-matasa-na-ha%C6%99ura-da-karatun-boko-saboda-rashin-tabbas-kan-samun-aiki?GJlXzGgqHj)

_2026-05-19 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matasa a baya-bayan na ke haƙura da ilimin boko saboda shakku kan yiwuwar samun aikin yi. Matsalar rashin aikin yi bayan shafe tsawon shekaru ana karatu tare da kashe maƙuden kuɗaɗe ya sanya matasa da dama musamman waɗanda ba ƴaƴan wasu ba ajje tunanin karatu tare da mayar da hankali a kasuwanci da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG-SCI_AND_TECH.mp3?guid=d2398d58-535e-11f1-a9c2-f70a09b3638e&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda harin dakarun Najeriya ya kashe ɗimbin mutane a kasuwar Zurmi](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260516-yadda-harin-dakarun-najeriya-ya-kashe-%C9%97imbin-mutane-a-kasuwar-zurmi?GJlXzGgqHj)

_2026-05-16 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' yana bita ne na mahimman labaran al'amura da suka wakana a makon da ya gabata. a wannan makon shirin ya soma ne daga Najeriya inda a farkon makon da ya wuce wani harin da dakarun Najeriya suka kai ta sama a kasuwar Tumfa ta karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamafara ya hallaka akalla mutum dari 100 tare da jikkata wasu da dama. Wannan harin da ke zaman mafi muni da dakarun…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/FOCUS-MAG-2026-05-16-OUMAROU.mp3?guid=a9269ad2-5101-11f1-bdb2-b74773a5b14a&source=GJlXzGgqHj)

## [An yafe wa ɗaliban da ke son shiga kwalejin ilimi rubuta JAMB a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260512-an-yafe-wa-%C9%97aliban-da-ke-son-shiga-kwalejin-ilimi-rubuta-jamb-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-05-12 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A yau muna ɗauke da wani labari mai daɗi ga ɗaliban da ke sha’awar zama malamai da kuma masu son shiga Kwalejin Ilimi a faɗin Najeriya. Gwamnatin ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin sauƙaƙa wa ɗalibai hanyar neman ilimi da kuma ƙarfafa musu gwiwa ta fuskar kuɗi. Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya sanar da cewa ɗaliban da ke son shiga Kwalejin Ilimi yanzu ba sai sun rubuta jarrabawar UTME ba.…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG-SCI-AND-TECH-2026-05-12.mp3?guid=9d1f2112-4ded-11f1-aa3f-5552ca60e7a4&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda al'ummar wani gari suka riƙe Al'adar da suke kira da "Sai kowa ya zo"](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260512-yadda-al-adar-sai-kowa-ya-zo-ke-samun-%C6%99arbuwa-a-arewacin-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-05-12 · Al'adun Gargajiya_

Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako tare da Abdoulaye Issa ya yi duba kan wata Al'ada da ake kira "sai kowa ya zo" a tsakanin al'ummar wani gari da ke Yankin Arewacin Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani.......

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG_AL_ADU_SAI_KA_ZO_2026-05-12___OK_wav.mp3?guid=407388ec-4de1-11f1-81c5-c5cc1f66516a&source=GJlXzGgqHj)

## [Wasu daga cikin muhimman labaru a cikin makon daya gabata](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260509-yadda-rikicin-cikin-gida-na-sauran-jam-iyu-a-najeriya-suka-%C9%97auki-hankali?GJlXzGgqHj)

_2026-05-09 · Mu Zagaya Duniya_

A wannan mako shirin zai mayar da hankali akan batun zabukan fidda gwani na Jam'iyar APC mai mulki a Najeriya da kuma rikicin cikin gida a sauran jam'iyun ƙasar suka ɗauki hankulan al'uma.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/FOCUS-INTERNATIONAL-ABDOULKARIM-2026-05-09.mp3?guid=76a8299e-4bd0-11f1-a7eb-1dbd3540f978&source=GJlXzGgqHj)

## [Tasirin karance-karance Littattafan Hausa wajen ɗabbaƙa al'adun Hausawa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260505-tasirin-karance-karance-littattafan-hausa-wajen-%C9%97abba%C6%99a-al-adun-hausawa?GJlXzGgqHj)

_2026-05-05 · Al'adun Gargajiya_

Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan tasirin karance-karancen Littattafan Hausa a zamantakewar Al'ummar yankin. Irin waɗannan Littafai kuwa sun ƙunshi Magana Jari da jiki Magayi baya da Uwar Gulma da Shehu Umar kana Ruwan Bagaja, waɗanda dukkaninsu suka taimaka wajen fito da Al'adar Hausawa a fili. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG_AL_ADU-AL_ADAR_KARATUN_LITATTAFAN_HAUSA_2026-05-05.mp3?guid=a4a58c1a-485b-11f1-815a-db8df3912498&source=GJlXzGgqHj)

## [Tasirin fasahar zamani wajen bunƙasuwar aikin jarida](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260505-tasirin-fasahar-zamani-wajen-bun%C6%99asuwar-aikin-jarida?GJlXzGgqHj)

_2026-05-05 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin ranar ƴancin ƴan Jaridu ta duniya da ke gudana a kowacce ranar 3 ga watan Mayu, bikin da ke zuwa a wannan karon cikin wani yanayi da aikin na Jarida ke ganin koma baya. Akwai dai ƙorafe-ƙorafe daga sassa daban-daban kan yadda aikin na Jarida ke fuskantar barazana kodayake masu ruwa da tsaki a wannan…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/shamsiyya_mag.mp3?guid=089362f4-4859-11f1-8abc-ddfa24853b21&source=GJlXzGgqHj)

## [Shirin tambaya da amsa na wannan mako ci gaba ne kan illar cutar olsa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/tambaya-da-amsa/20260502-shirin-tambaya-da-amsa-na-wannan-mako-ci-gaba-ne-kan-illar-cutar-olsa?GJlXzGgqHj)

_2026-05-02 · Tambaya da Amsa_

A yau shirin tambaya da amsa zai fara ne da ci gaban bayanin da muka faro a makon da ya gabata akan cutar gyambon ciki. Ku danna alamar sauraro dimin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG_TAMBAY_DA_AMSA_REPEAT-2026-04-25_NASIRU_EDITED.mp3?guid=259e92a0-4602-11f1-9d08-452a10959936&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda haɗakar ƙungiyoyi suka ƙaddamar da farmaki a sassan Mali](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260502-yadda-ha%C9%97akar-%C6%99ungiyoyi-suka-%C6%99addamar-da-farmaki-a-sassan-mali?GJlXzGgqHj)

_2026-05-02 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin ya soma daga ƙasar Mali inda a ranar 25 ga watan Afrilun da mu kayi ban kwana haɗakar mayakan Abzinawa na FLA da na ƙungiya masu ikirarin jihadi ta JNIM suka ƙaddamar da mugayen hare-hare a garuruwa huɗu na ƙasar da suka haɗa da Sevare, Kidal, Gao da kuma Kati. A garin Kati da ke zaman babban sansanin sojin ƙasar ƴan bindigar sun yi amfani da motoci shake da bama-bamai da manyan bindigogi…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/FOCUS-MAG-2026-05-02-OUMAROU.mp3?guid=76432c9e-4601-11f1-9695-47ff6cb11d3d&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda makarantun tsangaya suka fara gauraya karatun addini da na Boko don tafiya da zamani](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260428-yadda-makarantun-tsangaya-suka-fara-gauraya-karatun-addini-da-na-boko-don-tafiya-da-zamani?GJlXzGgqHj)

_2026-04-28 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda makarantun tsangaya da na Islamiyya suka fara gauraya karatun addini da na zamani a ƙoƙarin da suke yi na tafiya da zamani da kuma amun tallafi daga gwamnatoci da manyan ƙungiyoyi na duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/MAG-SCI-AND-TECH-2026-04-28.mp3?guid=07e022bc-42ea-11f1-92f9-e93c308afa41&source=GJlXzGgqHj)

## [Shirin tambaya da amsa na wannan mako ya ɗora ne kan illar cutar gyambon ciki](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/tambaya-da-amsa/20260425-shirin-tambaya-da-amsa-na-wannan-mako-ya-%C9%97ora-ne-kan-illar-cutar-gyambon-ciki?GJlXzGgqHj)

_2026-04-25 · Tambaya da Amsa_

A yau shirin tambaya da amsa zai fara ne da ci gaban bayanin da muka faro a makon da ya gabata akan cutar gyambon ciki. Ku danna alamar sauraro dimin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/MAG_TAMBAY_DA_AMSA_2026-04-25_NASIRU_EDITED.mp3?guid=8834d5aa-4080-11f1-8e04-955f63da893b&source=GJlXzGgqHj)

## [Shirin mu zagaya duniya ya tattaro manyan labaran da suka faru a wannan mako](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260425-shirin-mu-zagaya-duniya-ya-tattaro-manyan-labaran-da-suka-faru-a-wannan-mako?GJlXzGgqHj)

_2026-04-25 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin mu zagaya duniya na wannan mako ya duba manyan labaran da suka faru cikin wannan mako, a sassan duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sani.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/FOCUS-MAG-2026-04-25-OUMAROU_EDITED.mp3?guid=ff95b9b2-407f-11f1-91bc-955f63da893b&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260422-yadda-mata-a-arewacin-najeriya-ke-ya%C6%99i-da-jahilci-don-tallafawa-ilimin-%C6%B4a%C6%B4ansu-kashi-na-2?GJlXzGgqHj)

_2026-04-22 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/MAG-SCI_AND_TECH.mp3?guid=8215ea58-3e2b-11f1-8cb6-d15a6591ecb6&source=GJlXzGgqHj)

## [Rawar da mayaƙa suka taka zamanin da a Masarautun ƙasar Hausa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/al-adun-gargajiya/20260421-tasirin-maya%C6%99a-a-masarautun-gargajiyar-%C6%99asar-hausa?GJlXzGgqHj)

_2026-04-21 · Al'adun Gargajiya_

Shirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda ya duba batun da ya shafi mazajen dauri, musaman mayaƙan gargajiya a wannan zamani, jaruman da ke ƙarƙashin inuwar sarakunan gargajiya. Duk inda akwai masarautun gargajiya an san su da tarin mayaƙa da ke yin tsarin daka a cikin kowane irin hali don kare su. Wannan tsarin ne da ya samo sali tun zamani da ake yaƙe-yaƙe…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/MAG_AL_ADU-MAHARBA_A_DAMAGARAM-ZINDER_2026--21.mp3?guid=0a0affe0-3d62-11f1-8c66-ed98d9d79d9f&source=GJlXzGgqHj)

## [Makomar masu shiga tsakani,kan neman ƙulla yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260418-makomar-masu-shiga-tsakani-kan-neman-%C6%99ulla-yarjejeniya-tsakanin-amurka-da-iran?GJlXzGgqHj)

_2026-04-18 · Mu Zagaya Duniya_

Mecece makomar ƙoƙari da masu shiga tsakanin, musamman Pakistan ke yi a kan neman ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran duba da tsaurin wasu ko da dama daga cikin sharuɗɗan da ɓangarorin biyu suka gabatarwa juna? Nura Ado Suleiman ke yi muku barka da sake haɗuwa cikin shirin Duniyarmu a Yau

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/MAG-DEBATE-US-IRAN-ISRAEL-HEZBOLLAH_CEASFIRE-NURA-2026-04-17.mp3?guid=06a479ec-3b43-11f1-b41b-27415a36ad5b&source=GJlXzGgqHj)

## [Tambaya da Amsa: Tasirin tsibirin Kharg ga tattalin arziƙin Iran](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/tambaya-da-amsa/20260418-tambaya-da-amsa-tasirin-tsibirin-kharg-ga-tattalin-arzi%C6%99in-iran?GJlXzGgqHj)

_2026-04-18 · Tambaya da Amsa_

Shirin Tambaya da Amsa tare da Nasiru Sani, bisa al'ada kan amsa dukkanin tambayoyin da masu sauraro kan aiko, kuma guda cikin tambayoyin da shirin ya amsa a yau shi ne tasirin tsibirin Kharg ga tattalin arziƙin Iran. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/MAG_TAMBAYA_DA_AMSA_2026-04-18_NASIRU.mp3?guid=5627133e-3b08-11f1-a3cf-1b03635667cd&source=GJlXzGgqHj)

## [Bitar Labaran mako: Iran ta amince da buɗe mashigin Hormuz ga jiragen kasuwanci](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260418-bitar-labaran-mako-iran-ta-amince-da-bu%C9%97e-mashigin-hormuz-ga-jiragen-kasuwanci?GJlXzGgqHj)

_2026-04-18 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin Mu zagaya duniya tare da Oumarou Sani, kamar yadda ya ke zuwar muku a kowannen mako, a wannan karon ma ya yi bita ne kan muhimman labaran da suka faru a makon da muke ban kwana da shi. Cikin jerin labaran da ke ƙunshe a wannan shiri, akwai yadda Iran ta amince da buɗe mashigin Hormuz bayan ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki 10 tsakanin Isra'ila da Lebanon. Wannan da sauran manyan…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/FOCUS-MAG.mp3?guid=bf4609da-3b06-11f1-8989-1b03635667cd&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260414-yadda-mata-a-arewacin-najeriya-ke-ya%C6%99i-da-jahilci-don-tallafawa-ilimin-%C6%B4a%C6%B4ansu?GJlXzGgqHj)

_2026-04-14 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A arewacin Najeriya, shigar mata makarantun yaki da jahilci ya fara ne a matsayin wani yunkuri na inganta rayuwar iyali da kuma tarbiyyar yara, inda mata da dama sun fahimci cewa rashin ilimi na hana su taimaka wa yaransu wajen karatunsu na zamani da kuma kulawa da lafiyarsu. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/MAG-SCI-AND-TECH-2026-04-14.mp3?guid=10e6bc0e-37eb-11f1-97f6-759ddea089c0&source=GJlXzGgqHj)

## [An cimma yarjejeniyar tsagaita wutar makwanni 2 tsakanin Amurka da Iran](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/mu-zagaya-duniya/20260411-mu-zagaya-gabas-ta-tsakiya-amruka-da-iran-sun-amince-da-tsagaita-wuta?GJlXzGgqHj)

_2026-04-11 · Mu Zagaya Duniya_

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' tare da Oumaru Sani, ya yi bitar wasu daga cikin muhimman labaru kan lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana, daga cikinsu kuma akwai yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki 14 da aka cimma tsakanin Amurka da Iran, bayan da ƙasar Pakistan ta shiga tsakani.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/FOCUS-MAG-2026-04-11-mp3.mp3?guid=8ebcd2b6-3580-11f1-9d48-552fb654d988&source=GJlXzGgqHj)

## [Illolin da ke tattare da makami ko makamashin Nukiliya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/tambaya-da-amsa/20260411-illar-dake-akwai-inhar-isra-ila-da-iran-suka-%C6%99addamar-da-hare-hare-akan-cibiyoyin-nukiliyar-juna?GJlXzGgqHj)

_2026-04-11 · Tambaya da Amsa_

Shirin 'Tambaya da Amsa' kamar yadda ya saba a kowane mako, ya tuntuɓi masana a kan wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana domin samun Ilimi a kan ƙarin bayanin da suke nema. Daga cikin tambayoyin kuma akwai neman sani a kan Illar da ke tattare da harba makaman Nukiliya ko kuma kai wa tashohin sarrafa makamashin Nukiliya farmaki.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/TAMBAYA_DA_AMSA_2026-04-11_NASIRU__edited_ok_mp3.mp3?guid=1853576c-3580-11f1-9d00-552fb654d988&source=GJlXzGgqHj)

