# ilimi (audio feeds) — RSS Amplifier

Recent posts from the 1 feeds in the RSS Amplifier directory that cover ilimi.

Page: <https://rssamplifier.com/topics/ilimi/audio>  
Feed: <https://rssamplifier.com/topics/ilimi/audio.md>

---

## [Yadda matasa suka ƙera jirgi maras matuƙi mai cin Kilomita 30 a Kano](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260818-yadda-matasa-suka-%C6%99era-jirgin-maras-matu%C6%99i-mai-cin-kilomita-30-a-kano?GJlXzGgqHj)

_2026-08-18 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin a wannan makon ya leka Kanon Najeriya, inda aka gano wani sabon tarihin bunkasar kimiyya da fasaha da matasan yankin ke jagoranta. Wannan gagarumar bajinta dai wani matashi Abubakar Waiya, wanda ya daɗe yana fafutukar kera na'urorin shawagi ne ya ƙera jirgi maras matuƙi domin taimakawa ɓangaren tsaro da kuma boma. Jirgin da ya kera a yanzu yana da ikon tashi da kansa har na tsawon kilomita…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202608/MAG-SCI-AND-TECH-2026-08-18.mp3?guid=206ebca2-9ade-11f1-9d85-d5a741bcbce0&source=GJlXzGgqHj)

## [Makomar ilimin yara a Kano na cikin halin rashin tabbas](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260714-makomar-ilimin-yara-a-kano-na-cikin-halin-rashin-tabbas?GJlXzGgqHj)

_2026-07-14 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin na wannan makon cigaba ne kan wanda muka gabatar a makon jiya, wanda ya gano yadda yara a wasu yankunan jihar Kano basa zuwa makaranta saboda yawon tallace-tallace domin tara kudin kayan ɗaki. Yayin da su kuma mazan suke diban yashi da fasa Dutse, da sunan wai su taso suna da sana'ar dogaro da kai. Yankunan da wannan lamari yafi kamari sun hada da Challawa, Kafin Maiyaki, Madobi, Gora, da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-SCI-AND-TECH-2026-07-14.mp3?guid=471fafce-7f62-11f1-a08a-45e43ba2eff1&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda makomar ilimin yaran karkara a Najeriya ke cikin rashin tabbas](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260708-yadda-makomar-ilimin-yaran-karkara-a-najeriya-ke-cikin-rashin-tabbas?GJlXzGgqHj)

_2026-07-08 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A wannan makon, shirin ya nufi yankunan karkara, inda inda gine-ginen makarantu ke ci gaba da kasancewa a matsayin kango, kasancewar babu dalibai. A wasu wuraren kuma, azuzuwan sun zama fanko, yayin da matasa da yara suka ƙaurace wa shiga, ‘yan mata na fita birni yin tallace-tallace, su kuma samari na dambatawa da aikin ƙwadagon fasa duwatsu da ɗiban yashi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202607/MAG-SCI-AND-TECH-2026-07-07.mp3?guid=4df503e4-7abc-11f1-ad90-8115b569da94&source=GJlXzGgqHj)

## [Taron ƙaddamar da littafin tarihi na wani fitaccen matashi a Kanon Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260630-taron-%C6%99addamar-da-littafin-tarihi-na-wani-fitaccen-matashi-a-jiha-kano?GJlXzGgqHj)

_2026-06-30 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan taron ƙaddamar da sabon littafin tarihin nan mai suna 'Mu San Magabata', wanda fitaccen matashin marubuci Kabiru Ahmad Kwalli ya rubuta da aka gudanar a jihar Kanon Najeriya. Taron ya haɗa masana, sarakuna, da ɗandazon al'umma domin duba yadda za a ceto tarihin ƙasar Hausa da ke shirin bacewa. Wannan littafi, kamar yadda masana da dama suka bayyana,…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SCI-AND-TECH-2026-06-30.mp3?guid=42c72b3a-746a-11f1-8632-8da6f2af1ad5&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda aka gudanar da taron manyan masana na duniya a birnin Lagos](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260623-yadda-aka-gudanar-da-taron-manyan-masana-na-duniya-a-birnin-lagos?GJlXzGgqHj)

_2026-06-23 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A wannan makon, shirin ya mayar da hankali ne kan babban taron ƙungiyar Lagos Studies Association karo na goma da aka kammala a ƙarshen mako, wanda ya saba haɗa masana, malaman jami'o'i, da masu bincike daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen waje domin tattauna halin da ilimi yake ciki a nahiyar Afirka cikin wannan ƙarni. Wannan taro, wanda aka kafa shi shekaru goma da suka gabata a birnin…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SCI-AND-TECH-2026-06-23.mp3?guid=0bed7bfe-6ee4-11f1-b94e-ed9400012577&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda talauci ke hana ɗalibai cikar burinsu](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260609-yadda-talauci-ke-hana-%C9%97alibai-cikar-burinsu?GJlXzGgqHj)

_2026-06-09 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi hasken rayuwa na wanna Mako ya mayar da hankali ne kan yadda matsin tattalin arziki ke tilstawa ɗalibai haƙura da cikar burinsu na karatu, don kawai neman abin kaiwa baka, a kowacce rana. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsioyya Haruna.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-CI-AND-TECH-2026-06-09.mp3?guid=e91467ec-63de-11f1-afbf-7be3d85db93d&source=GJlXzGgqHj)

## [Shirin kawar da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta na samun nasara a Jigawa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260602-shirin-mayar-da-yaran-da-ba-sa-zuwa-makaranta-ajujuwa-na-samun-kar%C9%93uwa-a-jihar-jigawa?GJlXzGgqHj)

_2026-06-02 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya sake waiwayar matsalar nan ce ta yawaitar yaran da ba za zuwa makaranta a arewacin Najeriya, batun da a fannin ilimi ke ci wa al’ummar yankin tuwo a ƙwarya. Masu iya magana dai na cewa ‘mai rai ba ya rasa motsi’ domin kuwa duk da girman da wannan matsala ta yi a Najeriya musamman ma yankin arewacin ƙasar, akwai waɗanda suka tashi tsaye wajen ganin sun…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202606/MAG-SCI_AND_TECH-NURA-2026-01-02.mp3?guid=2de1bef4-5e69-11f1-8a60-7567fe6d1d99&source=GJlXzGgqHj)

## [Ɗimbin matasa na haƙura da karatun boko saboda rashin tabbas kan samun aiki](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260519-%C9%97imbin-matasa-na-ha%C6%99ura-da-karatun-boko-saboda-rashin-tabbas-kan-samun-aiki?GJlXzGgqHj)

_2026-05-19 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matasa a baya-bayan na ke haƙura da ilimin boko saboda shakku kan yiwuwar samun aikin yi. Matsalar rashin aikin yi bayan shafe tsawon shekaru ana karatu tare da kashe maƙuden kuɗaɗe ya sanya matasa da dama musamman waɗanda ba ƴaƴan wasu ba ajje tunanin karatu tare da mayar da hankali a kasuwanci da…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG-SCI_AND_TECH.mp3?guid=d2398d58-535e-11f1-a9c2-f70a09b3638e&source=GJlXzGgqHj)

## [An yafe wa ɗaliban da ke son shiga kwalejin ilimi rubuta JAMB a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260512-an-yafe-wa-%C9%97aliban-da-ke-son-shiga-kwalejin-ilimi-rubuta-jamb-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-05-12 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A yau muna ɗauke da wani labari mai daɗi ga ɗaliban da ke sha’awar zama malamai da kuma masu son shiga Kwalejin Ilimi a faɗin Najeriya. Gwamnatin ta fitar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin sauƙaƙa wa ɗalibai hanyar neman ilimi da kuma ƙarfafa musu gwiwa ta fuskar kuɗi. Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya sanar da cewa ɗaliban da ke son shiga Kwalejin Ilimi yanzu ba sai sun rubuta jarrabawar UTME ba.…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/MAG-SCI-AND-TECH-2026-05-12.mp3?guid=9d1f2112-4ded-11f1-aa3f-5552ca60e7a4&source=GJlXzGgqHj)

## [Tasirin fasahar zamani wajen bunƙasuwar aikin jarida](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260505-tasirin-fasahar-zamani-wajen-bun%C6%99asuwar-aikin-jarida?GJlXzGgqHj)

_2026-05-05 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan bikin ranar ƴancin ƴan Jaridu ta duniya da ke gudana a kowacce ranar 3 ga watan Mayu, bikin da ke zuwa a wannan karon cikin wani yanayi da aikin na Jarida ke ganin koma baya. Akwai dai ƙorafe-ƙorafe daga sassa daban-daban kan yadda aikin na Jarida ke fuskantar barazana kodayake masu ruwa da tsaki a wannan…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202605/shamsiyya_mag.mp3?guid=089362f4-4859-11f1-8abc-ddfa24853b21&source=GJlXzGgqHj)

## [Reach prospects with real signals (Sponsored)](https://crawlproof.com/a/pAfSp5LSAA3l)

_2026-05-05 · **Sponsored**_

Find prospects talking about your problem and get context-backed moments to engage

## [Yadda makarantun tsangaya suka fara gauraya karatun addini da na Boko don tafiya da zamani](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260428-yadda-makarantun-tsangaya-suka-fara-gauraya-karatun-addini-da-na-boko-don-tafiya-da-zamani?GJlXzGgqHj)

_2026-04-28 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda makarantun tsangaya da na Islamiyya suka fara gauraya karatun addini da na zamani a ƙoƙarin da suke yi na tafiya da zamani da kuma amun tallafi daga gwamnatoci da manyan ƙungiyoyi na duniya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/MAG-SCI-AND-TECH-2026-04-28.mp3?guid=07e022bc-42ea-11f1-92f9-e93c308afa41&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu - kashi na 2](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260422-yadda-mata-a-arewacin-najeriya-ke-ya%C6%99i-da-jahilci-don-tallafawa-ilimin-%C6%B4a%C6%B4ansu-kashi-na-2?GJlXzGgqHj)

_2026-04-22 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon ci gaba ne kan yadda wasu daga cikin iyaye mata ke fafutukar neman ilimi a Kano, duba da yadda a wasu makarantu ake tambayar matakin karatunsu kafin ɗaukar yaran su a matsayin ɗalibai. Mafi yawan iyaye lamarin baya musu daɗi, wasu na zargin ƙin ɗaukar yaran, sai dai hanzarin shine sanin irin kulawar da ya kamata makarantun su baiwa yaran ne yasa suke…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/MAG-SCI_AND_TECH.mp3?guid=8215ea58-3e2b-11f1-8cb6-d15a6591ecb6&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda mata a arewacin Najeriya ke yaƙi da jahilci don tallafawa ilimin ƴaƴansu](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260414-yadda-mata-a-arewacin-najeriya-ke-ya%C6%99i-da-jahilci-don-tallafawa-ilimin-%C6%B4a%C6%B4ansu?GJlXzGgqHj)

_2026-04-14 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A arewacin Najeriya, shigar mata makarantun yaki da jahilci ya fara ne a matsayin wani yunkuri na inganta rayuwar iyali da kuma tarbiyyar yara, inda mata da dama sun fahimci cewa rashin ilimi na hana su taimaka wa yaransu wajen karatunsu na zamani da kuma kulawa da lafiyarsu. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/MAG-SCI-AND-TECH-2026-04-14.mp3?guid=10e6bc0e-37eb-11f1-97f6-759ddea089c0&source=GJlXzGgqHj)

## [Wani matashi ya yi nasarar ƙera jirgi marar matuƙi a jihar Kano](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260407-yadda-wani-matasa-ya-%C6%99ir%C6%99iri-jirgi-marar-matu%C6%99i-a-jihar-kano-da-ke-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-04-07 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi Haske Rayuwa na wannan makon, ya yi dubi ne kan yadda wani matashi a jihar Kanon Najeriya ya ja hankalin jama’a, bayan ƙirƙirar jirgi maras matuƙi, daidai lokacin da matasan wannan ƙasa ke faɗi tashin yadda za su samo masu ɗaukar nauyin ayyukan fasahar da suke son cimmawa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruwa...........

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202604/MAG-SCI-AND-TECH-2026-04-07.mp3?guid=f9f629e8-3255-11f1-98ef-79af221ba259&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda wasannin na'ura kwamfita ke samun karɓuwa a tsakanin matasa](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260331-yadda-wasannin-na-ura-kwamfita-ke-samun-kar%C9%93uwa-a-tsakanin-matasa?GJlXzGgqHj)

_2026-03-31 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirimmu na ilimi hasken rayuwa na wannan mako yayi karin bayani akan wasannin na’ura kwamfuta masu kama da gaske da aka fi sani da virtual reality a turance. Danna alamar sauti domin sauraron karin bayani........

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202603/SCIENCE_TECH_MAGAZINE_ON_VIRTUAL_REALITY-_29-03-2026.mp3?guid=4f7e8c88-2ce4-11f1-8eed-79ca491f4bd4&source=GJlXzGgqHj)

## [Tasirin faɗowar wasu sinadarai daga sama a fagen kimiyya da fasaha](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260303-tasirin-fa%C9%97owar-wasu-sinadarai-daga-sama-a-fagen-kimiyya-da-fasaha?GJlXzGgqHj)

_2026-03-03 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin "Ilimi Hasken Rayuwa" na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya yada zango ne a Jamhuriyar Nijar inda abaya-bayan nan aka rika samun fadowar wasu abubuwa daga sararin samaniya, lamarin da ke ci gaba da faruwa a sassan a kasar. A baya bayan ne dai wasu abubuwa suka fado daga sararin samaniya a kauyuka 5 daban daban a yankin Kornaka, da Dakwaro da suka hada da Dan Madi, Baushi, da sauransu,…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202603/MAG_SHAMS_0303.mp3?guid=8386cb1a-16e8-11f1-83b7-a7999cc78106&source=GJlXzGgqHj)

## [Ra'ayoyi sun banbanta kan amfani da fasahar AI wajen yin tiyata](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260224-ra-ayoyi-sun-banbanta-kan-amfani-da-fasahar-ai-wajen-yin-tiyata?GJlXzGgqHj)

_2026-02-24 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako a wannan makon, ya mayar da hankali kan binciken da ya gano cewa shigar fasahar AI cikin fannin tiyata na haifar da wasu matsaloli masu kama da barazana ga rayuwar ɗan adam, kan haka ne ma muka zanta da masana a fannin kimiyya da kuma ɓangaren lafiya, inda muka jiyo ra’ayoyin mutane game da yadda wasu ke yarda AI ya duba lafiyarsu…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202602/MAG-SCI-AND-TECH-2026-02-24.mp3?guid=bd37884a-1161-11f1-9e3e-ddff297dda6e&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda satar jarabawa ke taka rawa wajen kassara ingancin ilimi a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260217-yadda-satar-jarabawa-ke-taka-rawa-wajen-kassara-ingancin-ilimi-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-02-17 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda satar jarabawa ke ƙoƙarin zama ruwan dare a makarantun sassan Najeriya, matsalar da ke ci gaba da illa ga ingancin ilimi a dukkan makarantu na ƙasar. Akwai zarge-zargen da ke nuna cewa wasu daga cikin jami'an hukumomin da ke kula da shirya jarabawa a matakai daban-daban na taimakawa wannan mummunar…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202602/MAG-SCH-AND-TECH-2026-02-17.mp3?guid=0efda242-0bde-11f1-85dd-1358074cc144&source=GJlXzGgqHj)

## [Yadda masu larurar ji ke fama da ƙalubalen karatu a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260210-yadda-masu-larurar-ji-ke-fama-da-%C6%99alubalen-kararun-karatu-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-02-10 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin na wannan mako ya ba da hankali ne akan yadda masu fama da larurar ji ke fama da ƙalubalen karatu a wasu sassan Najeriya.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202602/MAG-SCI-AND-TECH-2026-02-10.mp3?guid=1e77a130-0672-11f1-bec6-e78e88d0b892&source=GJlXzGgqHj)

## [Ana fuskantar koma bayan koyan harshen larabci a arewacin Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260203-ana-fuskantar-koma-bayan-koyan-harshen-larabci-a-arewacin-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-02-03 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali ne kan dalilan da suka haddasa rashin koyon ingantaccen larabci tsakanin daliban sakandare a arewacin Najeriya, sabanin lokutan baya. A shekarun baya, alkaluma sun nuna cewa kusan kaso hamsin na larabcin da Dalibai ke koya suna samun sa ne a makarantun boko ba lallai sun sun halarci makarantun Arabiya, al’amarin…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202602/MAG-SCI-AND-TECH-2026-02-03.mp3?guid=20128e46-00ec-11f1-86f0-9933e99ec2ac&source=GJlXzGgqHj)

## [Zero-Persistence E2EE (Sponsored)](https://crawlproof.com/a/zdsZBh2nTEcd)

_2026-02-03 · **Sponsored**_

End-to-end encryption with client-side WebCrypto and volatile memory.

## [Yadda satar jarabawa da cin hanci da rashawa ke kassara ɓangaren Ilimi a Kamaru](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260127-yadda-satar-jarabawa-da-cin-hanci-da-rashawa-ke-kassara-%C9%93angaren-ilimi-a-kamaru?GJlXzGgqHj)

_2026-01-27 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda wani bincike can a Jamhuriyyar Kamaru ya gano yadda satar Jarabawa da cin hanci da rashawa ke mummunan tasiri a ɓangare ilimin ƙasar. Matsalar ta cin hanci da rashawa kai tsaye ta yi mummunar illa ga yanayin ɗaukar malamai aiki da gina makarantu ko kuma samar da ci gaba a ɓangaren na Ilimi, yayinda a…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202601/MAG-SCI-AND-TECH-2026-01-27.mp3?guid=9fc7fcce-fb5c-11f0-aa9e-3d70584edd1c&source=GJlXzGgqHj)

## [Makomar karatu a yankin arewacin Najeriya cike da barazanar ƴanbindiga](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260120-makomar-karatu-a-yankin-arewacin-najeriya-cike-da-barazanar-%C6%B4anbindiga?GJlXzGgqHj)

_2026-01-20 · Ilimi Hasken Rayuwa_

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan makomar karatun ɗalibai a makarantun Najeriya musamman yankin arewaci mai fama da matsalolin tsaro, dai dai lokacin da aka koma sabon zangon karatu Iyaye na cike da fargaba kan tsaro a makarantu. Makwanni gabanin tafiya hutun zangon da ya gabata cikin watan Nuwamban bara ne, hare-haren ƴan bindiga suka…

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202601/MAG_SHAMS.mp3?guid=ad256c48-f5db-11f0-9fb8-b5fa733b00b2&source=GJlXzGgqHj)

## [Kashi na biyu kan yadda sabuwar manhajar fassarawa da lissafa haraji ke amfani a Najeriya](https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/ilimi-hasken-rayuwa/20260106-kashi-na-biyu-kan-yadda-sabuwar-manhajar-fassarawa-da-lissafa-haraji-ke-amfani-a-najeriya?GJlXzGgqHj)

_2026-01-06 · Ilimi Hasken Rayuwa_

A kashi biyu na shirin ilimi hasken rayuwa, mun ɗora kan sabuwar manhajar fassarawa da da sauƙaƙa lissafin karɓar haraji. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Faruk Yabo.

[Listen](https://audio.audiomeans.fr/pfx/b035a7c4-de15-11ef-9e7b-cfc4fb0c91f4/aod-rfi.akamaized.net/rfi/haoussa/audio/modules/actu/202601/MAG-SCIENCE_AND_TECH-2026-0501_FARUK_YABO.mp3?guid=f3048f78-eae1-11f0-a2ed-4f123c88bc39&source=GJlXzGgqHj)

