# akth (blogs) — RSS Amplifier

Recent posts from the 1 feeds in the RSS Amplifier directory that cover akth.

Page: <https://rssamplifier.com/topics/akth/blogs>  
Feed: <https://rssamplifier.com/topics/akth/blogs.md>

---

## [Kano: An yi jana&#8217;izar Almajirai 4 da suka rasu bayan cin wani abinci](https://www.hausa.ahsantnews.com.ng/kano-an-yi-janaizar-almajirai-4-da-suka-rasu-bayan-cin-wani-abinci/)

_2026-08-17 · ahsant · Ahsant Hausa_

An gudanar da jana’izar wasu yara Almajirai guda hudu wadanda suka rasu sakamakon cin wani abinci da ake zargin cewa gurbatacce ne. Shugaban ƙungiyar Tsangaya Media Network ta Najeriya Alaramma Malam Sani Musa Nuhu, ne ya tabbatar hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar. Ya ce, Almajiran huɗu sun kasance yan Tsangayar Malam Iliyasu \[…\]

## [Gwamna Abba Kabir ya amince da ƙarin albashi ga ma’aikatan Jami&#8217;o&#8217;in Northwest da Wudil](https://www.hausa.ahsantnews.com.ng/gwamna-abba-kabir-ya-amince-da-%c6%99arin-albashi-ga-maaikatan-jamioin-northwest-da-wudil/)

_2026-08-10 · ahsant · Ahsant Hausa_

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da sabon tsarin ƙarin albashi ga malaman jami’a da ma’aikatan da ba malamai ba na Jami’ar Aliko Dangote ta Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, da Jami’ar Northwest da ke Kano. Sabon tsarin albashin ya samo asali ne daga tsarin albashin da gwamnatin tarayya ta amince da \[…\]

## [Muna kira ga Sarkin Takutahar ƙasar Hausa ya yi duk abinda ya kamata don kawo wa Najeriya ci gaba– Sarkin Daura](https://www.hausa.ahsantnews.com.ng/muna-kira-ga-sarkin-takutahar-%c6%99asar-hausa-ya-yi-duk-abinda-ya-kamata-don-kawo-wa-najeriya-ci-gaba-sarkin-daura/)

_2026-08-07 · ahsant · Ahsant Hausa_

Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Dakta Umar Farouk, ya buƙaci Sarkin Takutahar Ƙasar Hausa Sheikh Abdulkadir Jiyali ya yi dukkan abinda ya kamata domin kawo wa Najeriya ci gaba. Sarkin na Daura ya bukaci hakan ne lokacin da yake nada shi a Matsayin Sarkin Takutahar Kasar Hausa na farko a tarihin Masautun Kasar Hausa a \[…\]

## [Da ɗumi-ɗumi: Gwamnatin Kano ta bada umarnin kulle asibitoci marasa Rijista](https://www.hausa.ahsantnews.com.ng/da-%c9%97umi-%c9%97umi-gwamnatin-kano-ta-bada-umarnin-kulle-asibitoci-marasa-rijista/)

_2026-07-30 · ahsant · Ahsant Hausa_

Gwamnatin jihar Kano ta ƙarkashin ma’aikatar lafiya, ta umarci hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu PHIMA, da ta kulle dukkan wani asibitin kuɗi da ke yin aiki ba tare da ya yi Rijista ba. Kwamishinan lafiya Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bada wannan umarni yayin da ya ke buɗe taron bita da bada \[…\]

## [Zaɓen 2027: KOMC da Gidauniyar AMG sun horas da ƴan jarida kan ɗakko rahoto yayin zaɓe](https://www.hausa.ahsantnews.com.ng/za%c9%93en-2027-komc-da-gidauniyar-amg-sun-horas-da-%c6%b4an-jarida-kan-%c9%97akko-rahoto-yayin-za%c9%93e/)

_2026-07-29 · ahsant · Ahsant Hausa_

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya NUJ sashen ƙungiyar masu yaɗa labarai ta ƙafar Internet (KOMC) tare da haɗin gwiwar Aminu Magashi Garba (AMG) Foundation, sun shirya taron horaswa na kwana guda domin ƙarfafa ƙwarewar ‘yan jarida kan yadda za su gudanar da rahotannin zaɓe cikin gaskiya, adalci da bin ƙa’idojin aikin jarida, tare da kare \[…\]

## [Rundunar soji na neman jami&#8217;in ta ruwa a jallo bisa zarginsa da sayar wa yan ta&#8217;adda Kaki](https://www.hausa.ahsantnews.com.ng/rundunar-soji-na-neman-jamiin-ta-ruwa-a-jallo-bisa-zarginsa-da-sayar-wa-yan-taadda-kaki/)

_2026-07-23 · ahsant · Ahsant Hausa_

Rundunar sojoji ta Nigerian Army Ordnance Corps NAOC ta ayyana wani jami’inta mai suna Mohammed Yusuf Amutu, a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo, bisa zarginsa da sayar da kayan sojoji, musamman kakin soja, ga ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka. Wannan na cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulɗa da jama’a \[…\]

## [Karin yan Najeriya 40 sun sauka a Lagos bayan kwaso su daga Afirka ta Kudu](https://www.hausa.ahsantnews.com.ng/karin-yan-najeriya-40-sun-sauka-a-lagos-bayan-kwaso-su-daga-afirka-ta-kudu/)

_2026-07-12 · ahsant · Ahsant Hausa_

Wasu ’yan Najeriya 40 da aka kwaso daga kasar Afirka ta Kudu sun isa filin jirgin sama na birnin Lagos. Hakan ya tabbatar da cewa, jimillar mutanen da aka dawo da su a rukuni na shida ya zama mutane 1,174. Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM) ta ce mutanen sun isa ne cikin \[…\]

## [INEC ta ƙara wa’adin miƙa ma ta sunayen ƴan takara](https://www.hausa.ahsantnews.com.ng/inec-ta-%c6%99ara-waadin-mi%c6%99a-ma-ta-sunayen-%c6%b4an-takara/)

_2026-07-12 · ahsant · Ahsant Hausa_

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta sanar da ƙara wa’adin da ta bai wa jam’iyyu na gabatar ma ta da sunayen ‘yan takararsu na zaɓen 2027 da kwana uku. ta cikin wata sanarwa da INEC ta fitar, ta ce jam’iyyu yanzu suna da damar miƙa sunayen ‘yan takararsu har zuwa tsakar dare \[…\]

## [Jami’ar Northwest ta kafa kwamitin bincike kan zargin da ake yi wa ma&#8217;aikacinta](https://www.hausa.ahsantnews.com.ng/jamiar-northwest-ta-kafa-kwamitin-bincike-kan-zargin-da-ake-yi-wa-maaikacinta/)

_2026-07-10 · ahsant · Ahsant Hausa_

Jami’ar Northwest Kano, ta kafa kwamitin bincike kan zargin da ake yi wa wani ma’aikacinta Dakta Nasa’i Muhammad Gwadabe, na yunƙurin cin zarafin wata ɗalibar Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria MAAUN. A cikin wata sanarwa da jami’ar ta fitar yau Juma’a mai ɗauke dasa hannun shugaba sashe yaɗa labaranta Malam Abubakar Ibrahim. Ta \[…\]

## [A Friend Gave You $30 (Sponsored)](https://crawlproof.com/a/1aXekktglovs)

_2026-07-10 · **Sponsored**_

Sign up, deposit $5 within 30 days, and start investing with expert guidance.

## [Buɗaɗɗiyar wasiƙa ga Gwamna Abba da Grand Khadi kan Alaƙalin Kotun harabar Hisbah](https://www.hausa.ahsantnews.com.ng/bu%c9%97a%c9%97%c9%97iyar-wasi%c6%99a-ga-gwamna-abba-da-grand-khadi-kan-ala%c6%99alin-kotun-harabar-hisbah/)

_2026-06-11 · ahsant · Ahsant Hausa_

Buɗaɗɗiyar wasiƙa ga Gwamna Abba da Grand Khadi kan Alaƙalin Kotun harabar Hisbah mai shari’a Sani Tanimu. Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu Ya mai girma gwamna Kano mai adalci Alh Abba Kabir Yusuf da shugaban alkalan kotunan shari’ar Musulunci ta jihar kano Dakta Tijjani Yusuf Yakasai ina muku fatan alheri Allah ya kara muku lafiya da \[…\]

