RSS Amplifier

Podcast

Muhallinka Rayuwarka

Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

rfi.frSource feed ↗24 episodes

Live Last read · last published · next check

Written by

Latest episodes

Saves to your Listen queue, to pick up on another day or another device.

Ƙarancin yashin gini na haddasa rikici tsakanin jama'a da illa ga muhalli

A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan yadda aikin gine gine ke haddasa bukatar yashi wanda nemanshi ke zama matsala tsakanin jama'a, da kuma illa ga muhalli da wurin noma da hanyoyin ruwa da sauransu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

Play

Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalli

Shirin Muhallinka rayuwarka na wannnan mako tare da Nasiru Sani ya duba irin gudun mawar da ganzun daji ke bayarwa wajan kare muhalli daga matsalar sauyin yanayi Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

Play

Yadda dazuka ke taimakawa wajan kare muhalli

Shirin Muhallinka rayuwarka na wannan mako tare da Nasiru Sani ya duba irin gudun mawar da dazuka ke bayar wa wajan kare muhalli daga matsalar sauyin yanayi. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

Play

Matakan da manoman Nijar ke ɗauka a lokutan da aka fuskanci ƙarancin ruwan sama

A Jamhuriyar Nijar,manoman dai sun fara da taka tsan-tsan ne saboda tsila-tsillar saukar ruwan shukar da suke fuskanta da kuma yanda ake samun dogon lokaci kafin saukar wani ruwan bayan saukar na farko, abun dake sanya shukar da suka yi ta mutu a ɗan wani lokaci.

Play

Illolin karancin gonaki kusa da jama'a da yadda ya shafi burin bunkasa samar da abinci

Sau da dama, masu burin shiga harkokin noma a Nigeria kan canza tunaninsu, sakamakon rashin samun gonakin da za su noma kusa da gari, lamarin da kan tilasta su jingine aniyarsu ta yin noma. Gwamnatin Nigeria dai, ta sha kira ga ‘yan kasar da su koma gona, la’akari da yadda Allah ya albarkaci kasar da wadatattun filayen noma da kuma yanayi mai kyau da za a iya noma kowane irin nau’in kayan abinci.

Play

Matsalar ambaliyar ruwa da kan dagula lamuran al’uma a Najeriya

Kamar kowace shekara, a bana ma ana hasashen samun ambaliyar ruwa a wasu ƙasashen yammacin Afrika, inda akan samu rasa rayuka da dukiya mai tarin yawa. A Najeriya, an sha samun hasarar rayuka a sanadin matsalar ambaliyar ruwan, da kan rutsa da wasu yankunan ƙasar.

Play

Masana na ci gaba da tsoratar da al'umma game da illolin da ke tattare da gurɓatacciyar iska

A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan tasirin gurɓatacciyar iska ga lafiyar halittu da muhalli wato air pollution a turance. Iska na gurɓa ta ne ta hanyoyi da dama, kama daga hayaƙin na’urori wato injina a masana'antu, zuwa tarkacen bola ko kuma ƙone wasu abubuwa, wanda su ke kawo cikas ga yanayin muhalli tare kuma da kawo tazgaro ga lafiyar ɗan Adam.

Play

Kananan manoma a Najeriya na nan kan tsarin noma na kaka da Kakanni

A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan yadda har yanzu, kananan manoma a Nigeria na nan kan tsarin noma na Kaka da Kakanni, lamarin da ake gani yana hana ruwa gudu wajen tabbatar da cimma burin kasar na kasancewa mai dogaro da-kai a fannin samun wadatar abinci.

Play

Yawaitar takin jabu ya zamewa Manoman Najeriya ƙalubale a bana

Shirin 'Muhallinka Rayuwarka na wannan makon, ya tattauna ne da masu ruwa da tsaki kan sha'anin Noma, a kan matsalar yawaitar taki da kuma magungunan ƙwari na jabu, matsalar da ta zamewa manoman Najeriya ƙalubale babba a shekarar bana.

Play

Sauyin Yanayi ya jefa Manoma cikin ruɗani kan lokacin da ya dace su fara shuka

Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna na a kan yadda samun saukar Ruwan Sama na farko a bana ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani dangane da lokacin da ya dace su fara shuka. Wannan na zuwa ne a yayin da hukumar hasashen Yanayi ta Najeriya wato NIMET, da uma wasu masana ke gargaɗi game da yiwuwar ɗaukewar ruwan saman da wuri, lamarin da zai yi janyo tafka…

Play

Yadda saukar ruwan sama na farko ya jefa manoma cikin ruɗani

A yau wannan shiri zai ba da hankali ne akan yadda Ruwan sama na farko da aka samu a baya-bayan nan ya jefa manoma a jihohin Arewacin Najeriya cikin ruɗani da fargaba, yayin da hukumar hasashen yanayi ta ƙasa, NiMet, da masana ke gargaɗi game da tsagaitawar ruwan saman da wuri wanda zai iya lalata duk wani amfani da aka yi a wannan lokaci.

Play

Matsalar karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar iyalai a sassan Nigeria

Matsalar nan ta karancin tsaftataccen ruwa, na ci gaba da addabar miliyoyin iyalai a sassan Nigeria, kila ko saboda rashin samun damar jan ruwan famfo a gidajensu, ko kuma rashin samun ruwan daga hukumomin samar da ruwan famfo na jihohinsu, duk da makudan kudin da gwamnatocin jihohin ke warewa, da sunan samar da ruwa wa jama’arsu. Wannan matsala ba kawai ta tsaya kan iyalai da kan rasa ruwan…

Play

Karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma a jamhuriyar Nijar

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan mako zai maida hankali ne kan yanda ake karfafa gwiwa ga jama'a su koma noma don ita ce babbar hanyar dogaro da kai ta fuskar abinci. Tun bayan halin matsin da jama'ar Jamhuriyar Nijar suka shiga biyo bayan juyin milkin soja da ta haddasa karamcin da tsadar abinci a cikin kasar aka rika zaburar da mutane su kama aikin noma musamman abincin da aka shigo da shi…

Play

Matasan kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada suka kai rangadi a Nijar

A yau shirin zai leka jamhuriyar Nijar ne inda matasa daga kasashe 11 da ke cikin tsarin shingen kare Hamada da zaizayewar kasa don mayar da yankin tsanwa suka kai rangadi a Nijar musaman a Jihohi 5 na kasar da suka hada da Tillaberi Niamey, Dosso, Maradi da Zinder don duba irin cigaban da Nijar ta samu a wannan fannin da nufin kwaikwayonsa don kaddamar da shi a kasashensu.

Play

Dalilan da suka sanya Manoma Albasa a Nijar fuskantar ƙalubale a bana

Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon, ya yi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar, inda aka fuskanci ƙalubale kan noman Albasa a shekarar bana. Bayanai daga ƙasar ta Nijar na cewa a halin da ake ciki, Manoma da dama sun shiga halin ƙaƙa-ni-kayi saboda rashin samun kuɗaɗen shiga, la'akari da irin rawar da noman na Albasa ke taka wa wajen sama musu abin kashewa.

Play

Yadda sare itace a Nijar ke haifar da koma baya wajen samun amfanin gona

Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka a wannan makon ya yi duba ne kan yadda ake samu canjin yanayi ta hanyar saran icen "Gawo" barkatai daga Makiyaya da su kansu Manoman, wanda ake ganin ke haifar da koma baya wajen samun yalawar abinci kamar, bakamar yadda aka saba ba a shekarun baya a cikin gonaki na Jamhuriyar Nijar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson..........

Play

Hukumar NIMET ta yi hasashen samun saukar ruwa da wuri a daminar bana a Najeriya

Shirin ‘Muhalinka Rayuwarka’ a wannan makon ya yaɗa zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya mayar da hankali kan hasashen ruwan sama da Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya NIMET ta yi, gabanin kamawar daminar bana, inda ta bayyana cewa damina za ta sauka da wuri a jihohi irin su Kano da Niger da Rivers da wasu jihohi 12 na ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael…

Play

Yadda cutar tumatiri ta kasara manoma a wasu jihohin arewacin Najeriya

Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ tare da Michael Kuduson a wanan mako ya yi duba kan wata mummunar cutar tumatiri da ake kira Tuta Absoluta ko kuma cuta mai karya garkuwar tumatir. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....

Play

Dalilan da masana suka ce su ke ƙara bayyana sauyin yanayi

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne kan yadda sauyin yanayi ko dai na zafi ko na sanyi ko kuma damina ke bayyana ƙarara, musamman a yankin yammacin Afirka. Ga misali a Najeriya, ɗaya daga cikin sauye-sauyen yanayin da aka shaida shi ne rashin hunturu a shekarar bana, musamman a Yankin arewacin ƙasar, inda aka saba ganin kankamar Yanayin na sanyin mai tsanani daga ƙarshen…

Play

Noman rani na fuskanta barazana a Najeriya sabida tsadar kayan noma irinsu taki

Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka’ a wannan makon ya yaɗa zango ne Tarayyar Najeriya, inda ya duba irin barazanar da noman rani ke fuskanta, musamman a wannan lokaci da farashin kayyakin gona suka faɗi warwas a yayin da farashin taki da sauran mahimman kayakin da ake amfaani da su wajen noman suke a can ƙololuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Michael Kuduson..........

Play

Yadda manoman Jamhuriyar Nijar ke fama da ɓarnar makiyaya a ƙarshen damina

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan karon zai mayar da hankali ne kan irin fama da ake sha a karshen damina tsakanin manoman da suke tattarar Kayan gona da makiyayan dake dawowa daga kiwo zuwa wuraren da ake aikin noman a wasu sasaan Jamhuriyar Nijar. A duk karshen damana makiyayan da suka tafi mashekari wurin kiwon dabbobinsu inda ke da isassar ciyawa nesa da gonaki na sabkowa wuraren da ake…

Play

Abubakar Ibrahim kan taron sauyin yanayi na COP30 da ke gudana a Brazil

An buɗe taron Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi da ake kira COP 30 a Brazil inda masana muhalli da sauyin yanayi daga kasashen duniya za su mayar da hankali da kuma samar da dabaru kan sauyin yanayi. Za'a kwashe makwanni biyu ana gudanar da wannan taro wanda zai mayar da hankali a kan ci gaba ko akasin haka da aka samu a kan wannan matsala.

Play

Yadda wani ruwa da ke ɓulɓulowa ta ƙasa ke zubar da gidaje da kashe bishiyu a Nijar

Shirin muhallinka rayuwarka na wannan yau zai maida hankalin ne kan wani ruwan dake bullowa daga kasa Wanda ya yi sanadiyar zubewar gidaje da kashe bishiyoyi da ga gurbata hanyoyi a unguwar Garin Malam ta Damagaram a Jamhuriyar Nijar. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.

Play

Barazanar wutar daji da ke lakume gonakai a Jamhuriyar Nijar

A cikin wannan shirin ,za mu leko Jamhuriyar Nijar inda a duk shekara ake fuskantar barazanar wutar daji da ke lakume gonakai da cimaka. Hukumomin Nijar sun dau matakai domin kawo karshen wannan al'amari da manoma da kuma jama'a ke kuka a kai.

Play