RSS Amplifier

Blog

fitacciya

fitacciya.com.ngSource feed ↗10 posts

Overdue Last read · last published · next check
Last read 8 hours ago, longer than this feed's 2 hours schedule.

Latest posts

Fagge ya nemi Ministan Shari'a ya shiga tsakani kan tsare Maryam Shehu

Lauyan kare hakkin ɗan Adam, Abba Hikima Fagge, ya yi kira ga Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya da ya shiga tsakani kan tsare Maryam Isah Shehu, wadda ya ce Hukumar EFCC ta shafe kwanaki 35 tana tsare da ita kafin daga bisani ta shigar da ƙara mai zargi ɗaya a kanta. Fagge ya bayyana cewa, Maryam, ɗalibar shekarar ƙarshe a Jami’ar Bayero Kano (BUK), ta shafe kwanaki 35 a hannun EFCC, duk da cewa…

Ambaliya ta lalata gidaje da gonaki a Neja

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje, wuraren kiwon kifi da kuma manyan gonaki a garin Muye da wasu unguwannin da ke kusa da shi a Ƙaramar Hukumar Lapai ta Jihar Neja. Fitacciya ta rawaito cewa, ambaliyar ta faru ne bayan Kogin Gurara ya cika sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a wannan daminar. Etsu Muye, Alhaji Salihu Muhammadu, ya bayyana cewa ambaliyar ta kuma mamaye kasuwanni tare da katse…

Atiku ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur idan ya ci zaɓe

Atiku ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur idan ya ci zaɓe Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasar Najeriya a 2027. Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake bayyana manufofinsa da shirinsa na tafiyar da ƙasar idan ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa…

Gwamnatin Kano ta bayyana makomar aikin titin Danbare

Aƙalla mutane 32 ne ake zargin ’yan bindiga suka kashe a ƙauyen Ungushi da ke Ƙaramar Hukumar Kebbe a Jihar Sakkwato, bayan wani mummunan hari da suka kai yankin. Fitacciya ta rawaito cewa, maharan sun kuma ƙona gidaje bakwai, shaguna biyu da motoci uku, yayin da ruwan sama ya hana gobarar yin ɓarna mai yawa, kamar yadda Aminiya ta ruwaito. Wani shugaban ƙauyen da ya shaida harin ya ce ’yan…

’Yan bindiga sun kashe mutum 32 a ƙauyen Sakkwato

Aƙalla mutane 32 ne ake zargin ’yan bindiga suka kashe a ƙauyen Ungushi da ke Ƙaramar Hukumar Kebbe a Jihar Sakkwato, bayan wani mummunan hari da suka kai yankin. Fitacciya ta rawaito cewa, maharan sun kuma ƙona gidaje bakwai, shaguna biyu da motoci uku, yayin da ruwan sama ya hana gobarar yin ɓarna mai yawa, kamar yadda Aminiya ta ruwaito. Wani shugaban ƙauyen da ya shaida harin ya ce ’yan…

El-Rufai ya shigar da ƙarar Naira biliyan 10 kan ICPC

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da sabuwar ƙarar Naira biliyan 10 kan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka, ICPC, kan zargin hana iyalansa ganinsa yayin da yake tsare. Fitacciya ta rawaito cewa, El-Rufai ya shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1852/2026 a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar 13 ga Agusta, inda ya zargi ICPC da hana matarsa, Aichatou…

Atiku ya nemi Tinubu ya daina ɗora wa tsofaffin gwamnatoci laifin matsalar matatun mai

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ci gaba da danganta matsalolin matatun man fetur na Najeriya da gwamnatocin da suka gabata. Fitacciya ta rawaito cewa, Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Sadarwar Jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Lahadi, inda ya ce gwamnatin Tinubu ba za ta iya ci…

Kwankwaso ya ce be damu da kirana ‘tayar da tayar’ ga mataimakan shugaban ƙasa

Kwankwaso ya ce be damu da kirana ‘tayar da tayar’ ga mataimakan shugaban ƙasa. Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba ya damuwa da yadda ake kallon mataimakan shugaban ƙasa a matsayin ‘tayar da tayar’ da shugaban ƙasa ke amfani da shi idan akwai matsala. Fitacciya ta rawaito cewa, Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Hukumar…

Kwankwaso ya bayyana dalilin da ya sa ya amince ya zama mataimakin Peter Obi

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ya amince ya zama mataimakin Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ne saboda tabbatar da daidaiton ƙasa, adalci da kuma samar da sauyin dimokuraɗiyya a Najeriya. Fitacciya ta rawaito cewa, Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da ya halarci shirin tattaunawa na Hukumar Dillancin Labaran Najeriya a Abuja ranar Lahadi, inda ya ce…

Kwankwaso ya bayyana makomar Shekarau, Ganduje da Abba Yusuf a siyasar Kano

Tsohon Gwamnan Kano kuma Sanata, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa tsohon Gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, da tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf, sun kammala siyasarsu a jihar Kano. Fitacciya ta rawaito cewa, Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan makomar wasu daga cikin tsofaffin abokan siyasarsa da suka rabu da shi, inda ya ce nasarar siyasa da…